Azeem Ahmed Tariq ( Urdu ) (ya mutu a ranar 1 ga watan Mayu shekara ta 1993) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance Shugaban MQM (Muhajir Qaumi Movement). An kafa jam'iyyar ne don fafutukar kare hakkin Mohajir a Sindh, wadanda suka kasance baƙi ne daga Kasar Indiya a lokacin da Indo da Pakistan suka rabu .

Azeem Ahmed Tariq
Rayuwa
ƙasa Pakistan
Harshen uwa Urdu
Mutuwa 1 Mayu 1993
Karatu
Harsuna Urdu
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Muttahida Qaumi Movement (en) Fassara

Kisan kai

gyara sashe

An kashe Tariq a gidansa na Karachi a ranar 1 ga watan Mayu, a shekara ta 1993. Da misalin karfe 3 na asuba, masu kutse sun shigo cikin gidan, sun dauki makullan dakin kwanan shi kuma sunyi ta harbi da yawa yayin da yake bacci a kasan dakin zane. Yana ɗaya daga cikin shugabannin MQM da ma'aikata waɗanda aka kashe tsawon shekaru.

Manazarta

gyara sashe