Ayuba Dauda
Ayub Daud (Somali, Larabci: أيوب داود ; an haife shi a ranar 24 ga watan Fabrairun shekara ta alif dubu ɗaya da dari tara da casa'in (1990)) Miladiyya. ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Somaliya wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ko mai kai hari ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Somaliya.
Ayuba Dauda | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Mogadishu, 24 ga Faburairu, 1990 (34 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Somaliya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 9 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 65 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 177 cm |
Aikin kulob
gyara sasheDan Daud Hussein, tsohon memba ne na tawagar kasar Somaliya, [1] An haifi Daud a Somalia, kuma ya koma Cuneo, Italiya tare da iyalinsa yana da shekaru biyar.[2][3]
Ya shiga sashin matasa na Juventus a cikin shekarar 2000 kuma ya fara halarta tare da tawagar Primavera (ƙasa da 20) a cikin kakar 2007-2008. Daud yana cikin tawagar Juventus a shekarar 2009 Torneo di Viareggio, inda aka yaba masa a matsayin daya daga cikin mafi kyawun 'yan wasan kwallon kafa na gasar. Ya zura kwallaye 20, kuma shi ne ya fi zura kwallaye a gasar.[4]
A ranar 14 ga watan Maris ɗin shekarar 2009, ya buga wasansa na farko tare da Juventus, ya maye gurbin Sebastian Giovinco a cikin mintuna na ƙarshe na nasarar Seria A 4-1 akan Bologna. [5]
A ranar 6 ga watan Agustan 2009, Daud ya bar Juventus kuma ya koma Crotone a matsayin aro. Matashin ya sha wahala a kulob din kudancin Italiya, kuma daga baya ya koma Juventus a watan Janairu na shekara mai zuwa. Sai aka mai dashi aro zuwa Serie C1 club Lumezzane. A ranar 25 ga watan Janairun 2011 ya tafi Gubbio a kan aro. Daud ya bar Italiya a watan Agustan 2013 ya koma kungiyar Budapest Honvéd Hungary.
Ƙwallayen ƙasa da ƙasa
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Size doesn’t matter for Ayub – The Star
- ↑ "Daud si ripete, la Juve piega il Parma" (in Italian). La Gazzetta dello Sport. 12 February 2009. Retrieved 14 March 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "AYUB DAUD" (in Italian). Calciomercato.it. 6 March 2009. Archived from the original on 9 March 2009. Retrieved 14 March 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "TMW VIAREGGIO – Juventus, Daud: una freccia bianconera" (in Italian). Juventus FC. 11 February 2009. Retrieved 14 March 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "JUVE-BOLOGNA 4–1: RIPRESA TRAVOLGENTE E L'INTER E' A −4" (in Italian). Calciomercato.it. 14 March 2009. Archived from the original on 16 March 2009. Retrieved 14 March 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)