Qamardeen Odunlami ( Larabci: قمر الدين‎ ; An haife shi 27 ga watan Agusta 1973)[1] wanda aka fi sani da sunansa Ayeloyun mawaƙin Musulunci ne kuma furodusa na Najeriya. Ya fitar da kundin wakarsa na farko Taqwallah a shekarar 1994 da kuma wani kundi na Igbeyawo wanda ya fito a shekarar 2003 wanda shi ne kundin wakarsa na 9 kuma ya taimaka wajen shahara da kuma haskakawa tauraron sa.

Ayeloyun
Rayuwa
Haihuwa 27 ga Augusta, 1973 (50 shekaru)
Sana'a
Sana'a mawaƙi

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

An haifi Ayeloyun a Agege, Legas, Najeriya su bakwai ne a gidan su. A 2006, ya samu damar ya karanci Sharia da Common Law a Jami'ar Ilorin, Jihar Kwara amma ya bar makarantar, inda ya mayar da hankali akan harkar Kiɗa.[2][3]

Aikin kiɗa gyara sashe

Tun yana ƙarami, Ayeloyun ya fara nazarin sha’awarsa ta waka a lokacin da yake karantarwa na Larabci da yamma a Marcaz, Agege inda ya rera waka a lokacin ramadam Laylatul Qadr saboda rashin samun ubannin gida a lokacin a makarantar Larabci.[4] Ya fara waka da fasaha a shekarar 1992 don magance wasu abun a Addini a Musulunci sannan ya fitar da albam dinsa na farko a shekarar 1994 kuma ya fitar da albam guda 25 gaba ɗaya.[5]

Nassoshi gyara sashe

  1. Adefaka, Bashir (3 June 2011). "I spent 18 months in my mother's womb – Aiyeloyun". Vanguard News (in Turanci). Archived from the original on 7 June 2011. Retrieved 2 October 2020.
  2. Admin (4 July 2014). "Day a fan kissed me in the public —Aiyeloyun". The Nation Newspaper (in Turanci). Archived from the original on 25 February 2018. Retrieved 2 October 2020.
  3. Owolabi, Abdullateef (26 May 2016). "About Alhaji Qamardeen Odunlami". ayeloyungloballink (in Turanci). Retrieved 2 October 2020.
  4. "I Still Want To Be A Lawyer – Islamic singer, Ayeloyun". Nigeria Films (in Turanci). Retrieved 2 October 2020.
  5. Admin (4 July 2014). "Day a fan kissed me in the public —Aiyeloyun". The Nation Newspaper (in Turanci). Archived from the original on 25 February 2018. Retrieved 2 October 2020.