Ayandiji Daniel Aina
Ayandiji Daniel Aina ɗan ƙasar Najeriya ne mai bincike kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Caleb, dake Jihar LegasNajeriya.[1]
Ayandiji Daniel Aina | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ibadan |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Ilimi
gyara sasheAyandiji ya sami digirin sa na farko wanda shine PG Diploma a aikin jarida daga Cibiyar Jarida ta Najeriya,[2] Ogba, Legas a shekara ta 1991. Ya yi karatun digirinsa na BA (Hons) a fannin Falsafa da Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Ibadan a shekarar 1988, daga nan kuma ya koma Jami'ar Ibadan a shekarar 1992 don yin digirinsa na biyu a fannin kimiyyar siyasa da kuma digiri na uku a fannin kimiyyar siyasa har ila yau a jami'a guda.
Sana'a
gyara sasheAyandiji kwararre ne kan harkokin yaɗa labarai tare da gogewar aiki (kimanin shekaru goma) tare da Kamfanin Diflomasiyya na Duniya da ke Legas da kuma Daily Times Plc ta Najeriya.[3]
A lokacin zamansa a Jami'ar Babcock, Aina ya zama Shugaban Sashen na tsawon wa'adi biyu a shekarun (1999-2003), Dean na Faculty of Management and Social Sciences a shekarun (2003-2006) bayan nan ya zama Shugaban Ma'aikata na Shugaban jami'a a shekarun (2006 – 2008), sannan ya bi kuma ya sami Dean of School of Postgraduate School a (2010 – 2011) bayan haka ya zama Dean Babcock Business School a shekarar (2013 – 2015). Ya kuma kasance Farfesa mai ziyarar kuma shugaban gidauniyar Sashen Kimiyyar Siyasa da Huldata Ƙasa da Ƙasa, Jami'ar Jihar Osun (2009). An naɗa shi a matsayin shugaban sabuwar Makarantar Kasuwanci ta Babcock bayan ya dawo daga Jami’ar Adeleke inda ya yi hidimar majagaba-Mataimakin Shugaban Jami’ar.[1]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheAddinin Ayandiji Kiristanci ne. Ya auri Rachael wacce Malamar Jami’a ce a fannin sarrafa albarkatun bayanai kuma yana da ‘ya’ya uku.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Caleb University ::: Vice Chancellor". calebuniversity.edu.ng. Archived from the original on 2018-04-11. Retrieved 2018-04-10.
- ↑ "Ayandeji".
- ↑ "Ayandeji".