Aurélie Adam Soule ko Aurélie Adam Soule Zoumarou (an haife ta a shekara ta 1984) 'yar siyasar Benin ce wacce ke aiki a matsayin Ministar Tattalin Arziki na Digital da Sadarwa a Majalisar Dokokin Benin.

Aurélie Adam Soule
Minister of Digital Technology and Digitalization (en) Fassara

27 Oktoba 2017 -
Rafiatou Monrou (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Nikki (en) Fassara, 1984 (40/41 shekaru)
ƙasa Benin
Karatu
Makaranta Syracuse University (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
hoton aurelie adam
hoton aurelir adam

Rayuwar farko da aiki

gyara sashe

An haifi Soule a Nikki a shekarar 1984. Tana da digiri na biyu a fannin fasaha daga Telecom SudParis da Certificate in Management of Public Policy and Leadership daga Jami'ar Syracuse a New York.[1] Ta yi aiki a Faransa kuma ta koma Benin a shekarar 2008.[1]

Aikin siyasa

gyara sashe

An naɗa Soule a matsayin Ministar Tattalin Arziki na Digital da Sadarwa na Benin.[1] a watan Oktoba 2017 na Shugaba Patrice Talon.[2]


A cikin watan Nuwamba 2018, Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ya naɗa Soule zuwa Kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Tallafin Kuɗi na Dijital na Manufofin Ci Gaban mai Dorewa, wanda Maria Ramos da Achim Steiner suka jagoranta. [3]

An zaɓi Soule ta zama shugabar ministocin ƙasashe masu magana da harshen Faransanci waɗanda ke aiki tare don inganta matsakaici da dogon zangonsu na tsare-tsaren tattalin arzikin dijital a shekarar 2019.[4] Soule ta ƙarfafa ƙarin ƙididdiga da UNCTAD ke tallafawa a Benin. An rubuta dokoki don daidaita tattalin arzikin e-economy amma ba a zartar da su ba. Soule ta lura cewa cutar ta kwalara a cikin shekarar 2020 ta ba da dama don ci gaba da kasuwancin e-commerce.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 "Aurelie Adam Soule Zoumarou". World Bank Live (in Turanci). 2019-10-15. Retrieved 2020-02-15.
  2. "Aurelie Adam-Soule Zoumarou". www.broadbandcommission.org. Archived from the original on 2020-02-15. Retrieved 2020-02-15.
  3. Task Force on Digital Financing of Sustainable Development Goals United Nations, press release of 29 November 2018.
  4. Rédaction, La. "Bénin : la ministre Aurélie Adam Soulé à la première réunion du Groupe de travail sur le numérique | CIO MAG" (in Faransanci). Retrieved 2020-02-15.
  5. "unctad.org | Benin, Mali and Niger eager to tap e-commerce opportunities". unctad.org. Retrieved 2020-05-21.