Anthony Effah

Dan siyaasan Ghana

Anthony Effah dan siyasan Ghana ne kuma dan majalisar wakilai ta bakwai a jamhuriyar Ghana ta hudu mai wakiltar mazabar Asikuma-Odoben-Brakwa a shiyyar tsakiya a kan tikitin New Patriotic Party.[1]

Anthony Effah
Member of the 7th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2017 -
District: Asikuma-Odoben-Brakwa Constituency (en) Fassara
Election: 2016 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 24 ga Janairu, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Ghana
Mazauni Yankin Tsakiya
Karatu
Makaranta University of Ghana Master of Business Administration (en) Fassara : finance (en) Fassara
University of Ghana Bachelor of Arts (en) Fassara : ikonomi
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Mai tattala arziki da Ma'aikacin banki
Imani
Addini Kiristanci
Jam'iyar siyasa New Patriotic Party

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

An haifi Effah a ranar 24 ga watan Janairun, shekara ta alif ɗari tara da sittin 1960 A.c)kuma ya fito ne daga Breman-Brakwa a yankin tsakiyar kasar Ghana. Ya yi digirinsa na farko a fannin tattalin arziki a shekarar 1985 sannan kuma ya yi digirinsa na farko a fannin harkokin kasuwanci (Finance) daga Jami'ar Ghana a 2003.[2]

Aiki gyara sashe

Effah shi ne Daraktan Gudanar da Hatsari da Biyayya a Bankin Fidelity da ke Accra.[2] Ya kuma kasance Shugaban Hukumar Gwamnonin Bankin Karkara na Brakwa-Breman.[3][4]

Siyasa gyara sashe

Effah memba ne na New Patriotic Party.[5] Ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Asikuma Odoben Brakwa a shiyyar tsakiya daga 2017 zuwa 2021.[2][6][7] Ya lashe zaben 'yan majalisar dokoki a babban zaben kasar Ghana na 2016 da kuri'u 23,760 ya samu kashi 50.1% na yawan kuri'un da aka kada yayin da dan takarar majalisar dokokin kasar NDC Alhassan Kobina Ghansah ya samu kuri'u 23,330 wanda ya samu kashi 49.2% na yawan kuri'un da aka kada, dan takarar majalisar dokokin jam'iyyar PPP Richard Ato Quinoo ya samu kuri'u 237 wanda ya zama kashi 0.5% na yawan kuri'un da aka kada sannan dan takarar majalisar CPP Hayford Amoakoh ya samu kuri'u 90 wanda ya zama kashi 0.2% na yawan kuri'un da aka kada.[8]

A shekarar 2019, ya kasance memba a kwamitin kudi.[9]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Effah Kirista ce.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. "Member of Parliament: HON. ANTHONY EFFAH". Parliament of Ghana. Retrieved 16 February 2019.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "Effah, Anthony". Ghana MPS (in Turanci). Retrieved 2022-11-24.
  3. "Brakwa-Breman Rural Bank makes impressive profit". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2022-11-24.
  4. "Brakwa Breman Rural Bank continues to grow significantly". BusinessGhana. Retrieved 2022-11-24.
  5. "Dr Bawumia Fulfills Promise To Zongo". DailyGuide Network (in Turanci). 2016-11-22. Retrieved 2022-11-24.
  6. "Breman Brakwa health centre in dire need of support". www.ghanadistricts.com. Retrieved 2022-11-24.
  7. 3news.com (2017-11-24). "Businesses advised to take advantage of Queen of Denmark's visit". 3News.com (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-03. Retrieved 2022-11-24.
  8. FM, Peace. "2016 Election - Asikuma Odoben Brakwa Constituency Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2022-11-24.
  9. "NPP MP Rubbishes Calls For Bi-Partisan Probe Into Menzgold Saga". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2022-11-24.