Anne-Marie Adiaffi
Anne-Marie Adiaffi (1951-1994) marubuciyar ƙasar Ivory Coast ce wacce ta yi suna a cikin shekarar 1983 tare da littafinta mai suna Une vie hypothéquée (Rayuwar jingina).[1][2]
Anne-Marie Adiaffi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Abengourou (en) , 21 ga Maris, 1951 |
ƙasa | Ivory Coast |
Mutuwa | Abidjan, 1994 |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci |
An haife ta a shekarar 1951 a Abengourou, Adiaffi ta yi karatu a makarantun Cote d'Ivoire kafin ta yi karatu a Marseille kuma a ƙarshe a Dakar, inda ta sami takardar shaidar difloma a matsayin sakatariyar harshe biyu. Bayan ta fara aiki a banki, ta shiga gidan wallafe-wallafen Novelles Éditions Africaines a cikin 1983. Bayan satiric Une vie hypothéquée, ta buga La ligne brisée (1989) game da wani mutum da aka kore shi daga ƙauyensa bayan rashin sa'a akai-akai. Ta rasu a birnin Abidjan a shekarar 1994.
Nassoshi
gyara sashe- ↑ Gikandi, Simon (2 September 2003). Encyclopedia of African Literature. Routledge. pp. 14–. ISBN 978-1-134-58223-5.
- ↑ "Anne-Marie Adiaffi" (in French). University of Western Australia. Retrieved 24 March 2015.CS1 maint: unrecognized language (link)