Aminu Ala

Marubuci kuma mawakin Hausa

Aminu Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da Alan Waƙa (an haife shi a ranar 11 ga watan Fabrairu, shekara ta 1973), mawaƙin Hausa ne kuma Mawallafin littattafai daga Jihar Kano ta Arewacin Najeriya.[1][2][3]

Aminu Ala
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 11 ga Faburairu, 1973 (51 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Hausa
Sana'a
Sana'a mawaƙi

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

Aminu Ala ya kammala karatunsa na firamare a makarantar firamare ta Tudun Murtala tsakanin shekara ta 1980 zuwa 1986, sannan kuma ya wuce GSS Kawaji Secondary School a Dakata Kano daga 1987 zuwa 1992 a 2004. Ya ci gaba da karatunsa a Makarantar Fasaha a Kano inda ya samu difloma a shekarar 2007.[4]

Littattafai

gyara sashe

An fara sanin Ala a fagen rubutun harshen Hausa kafin a san shi a fagen waka. Ala ya rubuta littattafai kusan tara ciki har da:[5]

• Cin Zarafi

• Bakar Aniya

• Sawaba

• Cin Fuska

• Jirwaye

• Tarzoma

• Diwanin Ala

Ala ya fara waƙa tun yana ɗalibi a makarantar Islamiyya a lokacin da ake koya musu addini da ilimi ta hanyar waka, ta yadda za su iya fahimta da tsarawa cikin sauki. A lokacin ne aka koya musu waƙoƙin yabo ga Annabi Muhammad, duk lokacin da watan Maulidi ya faɗi, Ala na cikin waɗanda suka hau mimbari a addinin musulunci, don karanta waƙoƙi. Ta haka ne ya cusa wa Ala sha’awar kiɗa.[6][7]

Bayan Ala ya girma sai ya fara ƙoƙarin rubuta waka.[8]

  1. "Hukumar fina-finan Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙi - Aminu Ala". BBC News Hausa. 2020-08-19. Retrieved 2021-04-05.
  2. "...Daga Bakin Mai Ita tare da Alan Waƙa". BBC News Hausa. 2020-12-17. Retrieved 2021-04-05.
  3. "Aminu Ladan Abubakar, Alan Waka: Gwarzonmu Na Mako". Leadership Hausa Newspapers (in Turanci). 2020-09-17. Retrieved 2021-08-06.
  4. "Kida da Al'adu - Tattaunawa da Alan Waka a Kano". RFI. 2014-03-09. Retrieved 2021-08-06.
  5. "Cikakken Tarihin Aminu Alan Waka" (in english). Retrieved 2021-04-05.CS1 maint: unrecognized language (link)
  6. Sani, Abu-Ubaida (2018-09-15). "Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) Na Salisu Ahmad YAKASAI Da Abu-Ubaida SANI". Medium (in Turanci). Retrieved 2021-04-05.
  7. Welle (www.dw.com), Deutsche. "Tarihin mawaƙi Abubakar Ladan Zariya | DW | 02.08.2010". DW.COM. Retrieved 2021-04-05.
  8. "Wakokin Aminu Ladan Abubakar, Alan Waka, Su Na Yin Kasuwa Sosai". VOA. Retrieved 2021-08-06.