Aminata Boureima Takoubakoyé
Aminata Takoubakoyé Takoubakoyé (an haifeta a ranar 23 ga Satumban shekarar 1979, a Niamey, Niger ) ƴar Nijar ce kuma ƴar siyasa. Tsakanin Fabrairun shekarar 2010 zuwa Afrilu 2011, Takoubakoyé ta jagoranci Ma'aikatar Sadarwa da Fasahar Sadarwa da Al'adu a cikin Gwamnatin Riƙon ƙwarya ta Rundunar Soja ta Majalisar Ƙoli don Maido da Dimokuraɗiyya.[1][2]
Aminata Boureima Takoubakoyé | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Niamey, 23 Satumba 1979 (45 shekaru) |
ƙasa | Nijar |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da Mai tattala arziki |
Sana'a
gyara sasheBayan dawowarta Nijar bayan ta yi karatu a Rabat, a Morocco, Aminata Takoubakoyé ta karɓi muƙamin ƙwararre a hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa a cibiyar ƙididdiga ta Nijar. Daga Afrilun Shekarar 2004 zuwa Satumba 2009, ta kasance Jami'ar Watsa Labarai da Taimako a Sakatariyar Dindindin na Tsarin Dabarun Rage Talauci (Secrétariat Permanent de la Stratégie de Réduction de la Pauvreté). Daga bisani, daga Satumba 2009 zuwa Maris 2010, Takoubakoyé ta kasance mai gudanarwa a National Observatory for Poverty (Observatoire National de la Pauvreté). A watan Maris na 2010, Janar Salou Djibo, babban kwamandan sojojin Nijar, ya naɗa ta a gwamnatin riƙon ƙwarya kuma ya ba ta amanar sashen sadarwa, sabbin fasahohin yaɗa labarai da al'adu. Ta riƙe ofishin har zuwa Afrilu 2011.[3]