Sarauniya Amina

turunku
(an turo daga Amina)

Sarauniya Amina Sarauniyar Zazzau, ta rayu daga shekara ta 1533 zuwa shekara ta 1610, ɗaya ce daga cikin yara biyu da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Wato ita Amina ɗin da kuma ƙanwarta mai suna Zariya. Ta yi sarautar Zazzau bayan rasuwar mahaifinta, daga shekara ta 1509 zuwa shekara ta 1522, wato shekarunta sha uku kenan a kan karagar mulki. Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, kuma ta shida (6) a cikin sarakunan haɓe waɗanda sukai mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau. Har ila yau a cikin jerin sarakunan Zazzau gaba ɗaya ita ce ta ashirin da uku.

Sarauniya Amina
Rayuwa
Haihuwa 1533
ƙasa Zazzau
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 1610
Karatu
Harsuna Hausa
Sana'a
Sana'a Jarumi
Imani
Addini Musulunci
Gunkin Sarauniya Amina da Doki

Ana kallon Sarauniya Amina a matsayin mace ƴar siyasa kuma ma’abociyar al’ada wacce tayi gagarumin mulki a ƙarni na sha shida a ƙasar hausa,[1] Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da Daular Usmaniyya ta mulka. Ta yi kaiwa da komowa na yaƙe-yaƙe a wurare da dama. Idan aka ɗauki tun daga Zariya har zuwa Abuja akwai ƙananan garuruwa da dama da sarauniya Amina ta kafa, sai dai ba masu girma ba ne, saboda kamar dai wurare ne da ta ci zango a wajen. Jarumtarta da ƙwazonta ya kasance abin jinjina ne a ƙasar Najeriya, Afirka da kuma duniya baki ɗaya.

Dangane da batun waje ko kuma garin da Sarauniya Amina ta rasu, a gaskiya babu tabbas, to amma masana tahiri suna kyautata zaton cewa ta rasu ne a can ƙasar Gara, wato ƙasar Igala kenan, wadda ke cikin Jihar Kogi a arewacin Najeriya a halin yanzu. Wannan dalili ne ma ya sa ba a san takamaiman inda kabarin Sarauniya Amina ya ke ba.

Idan aka koma ga maganar zuriyar sarauniya Amina, a gaskiya abu ne mai wuya ace ga waɗansu da suke zuriyarta ne, tun da a gaskiya yadda tarihi ya nuna, Sarauniya Amina har ta mutu ba ta yi aure ba. Don haka babu wata shaida dake nuna cewa a ciki ko wajen zazzau akwai wasu da za a iya cewa zuriyarta ne.

To sai dai duk da cewa, akwai bayanai masu sarƙaƙiya da kuma saɓani na masana tarihi a game da rayuwar sarauniya Amina, to amma dai magana mafi rinjaye ita ce; Sarauniya Amina ta taɓa wanzuwa a doron ƙasa a matsayin sarauniya a Zazzau.

Diddigin bayanai na waje

gyara sashe
  • Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.

Manazarta

gyara sashe
  1. Kabir, Hajara Muhammad.Northern women development. [Nigeria].p.110. ISBN 978-978-906-469-4.