Alice Teni Boon

'yar siyasan Ghana

Alice Teni Boon (An haife ta ranar 12 ga watan Janairu, 1962). ‘yar siyasa ce, ‘yar kasar Ghana wacce ta taɓa zama ‘yar majalisa mai wakiltar mazabar Lambussie daga shekara ta 1999 zuwa shekarar 2009.[1]

Alice Teni Boon
Member of the 4th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2005 - 6 ga Janairu, 2009
District: Lambussie Constituency (en) Fassara
Election: 2004 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the 3rd Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2001 - 6 ga Janairu, 2005
District: Lambussie Constituency (en) Fassara
Election: 2000 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the Parliament of Ghana (en) Fassara

1999 - 2009
Rayuwa
Haihuwa Lambussie (en) Fassara, 12 ga Janairu, 1962 (62 shekaru)
ƙasa Ghana
Karatu
Makaranta University of Ghana Master of Business Administration (en) Fassara : unknown value
University of Westminster (en) Fassara
University of Media, Arts and Communication Bachelor of Arts (en) Fassara : communication studies (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Malami da consultant (en) Fassara
Wurin aiki Lambussie Karni District
Imani
Addini Eastern Orthodoxy (en) Fassara
Jam'iyar siyasa National Democratic Congress (en) Fassara

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Boon a ranar (12) ga watan Janairu a shekara ta (1962). Ta halarci Jami'ar kasar Ghana da Jami'ar Westminster. Ta kuma halarci Cibiyar Nazarin Jarida ta Ghana da Kwalejin Pitman Central da ke Landan.

Daga nan ta samu digirin digirgir kan harkokin kasuwanci da kuma Master of Arts a fannin sadarwar jama'a. Babban karatunta ya kasance a fannin Sadarwa.[2]

Boon kwararriya ce a fannin sadarwa sannan kuma mai ba da shawara ta hanyar sana'a. Ita ma 'yar siyasa ce a jam'iyyar National Democratic Congress, jam'iyyar siyasar kasar Ghana.[2]

Alice ta shiga majalisar ne a kan tikitin takarar jam’iyyar NDC a ranar Talata( 8) ga watan Yunin a shekara ta( 1999), lokacin da ta lashe zaben fidda gwani a ranar( 26) ga watan Mayun a shekara ta (1999), bayan rasuwar Luke Koo, dan majalisar wakilai a lokacin.[3][4]

Daga bisani ta lashe kujerar a lokacin babban zaben watan Disamba na shekara ta (2000), da kuma na watan Disamba na( 2004), Sai dai ta rasa kujerar a hannun John Duoghr Baloroo na New Patriotic Party (NPP) a babban zaben watan Disamba na (2008), A lokacin babban zaben watan Disamba na (2012) , Edward K. Dery ya maye gurbinta wanda sakamakon haka ya lashe kujerar NDC.[5]

Zaben 2000

gyara sashe

An zabi Boon a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Lambussie a yankin Upper West na Ghana a babban zaben Ghana na shekara ta( 2000). Don haka ta wakilci mazabar a majalisa ta( 4), a jamhuriya ta 4 ta Ghana.[6]

An zabe ta ne da kuri'u( 7,076) daga cikin kuri'un da aka kada. Wannan yayi daidai da (60.80%) na jimlar ingantattun ƙuri'un da aka jefa. An zabe ta a kan David Mwinfor Deribaa dan takara mai zaman kansa, Kabiri Nmin na Jam'iyyar Reform Party, Ampulling Nicholas na New Patriotic Party da Bamie Mubashir Ahmed na United Ghana Movement Party. Wadanda suka samu kuri'u( 2,472), kuri'u( 1,272,), kuri'u( 441) , kuri'u( 375) da kuri'u bi da bi.[6]

Waɗannan sun yi daidai da( 60.80%, 21.20% , 10.90%, 3.80%, 3.20% da 0.00%), daidai da jimillar ƙuri'un da aka jefa. An zabi Boon a kan tikitin jam'iyyar Democratic Congress. Jam'iyyar National Democratic Congress ta lashe kujeru (7), na 'yan majalisa a yankin Upper West a zaben.[7]

Gaba daya jam'iyyar ta samu 'yan tsiraru na wakilai (89), daga cikin kujeru (200), na majalisar dokoki ta( 3) a jamhuriya ta( 4), ta Ghana.[7]

Zaben 2004

gyara sashe

An zabi Boon a matsayin yar majalisa mai wakiltar mazabar Lambussie a babban zaben Ghana na shekara ta ( 2004). Don haka ta wakilci mazabar a majalisa ta (4), a jamhuriya ta (4), ta Ghana. An zabe ta ne da kuri'u (6,554), daga cikin (12,480) da aka kada. Wannan yayi daidai da kashi (52.5%) na jimlar ingantattun ƙuri'un da aka jefa.[2][8][9]

An zabe ta a kan Thomas F. Bitie-Ketting na babban taron jama'a, Sebastian Koug Bamile na Sabuwar Jam'iyyar Patriotic da Abubakari Alhaji Yahaya na Jam'iyyar Convention People's Party.[8][9]

Wadannan sun samu kuri'u( 1,265,) kuri'u (4,553) da kuri'u( 108) bi da bi. Waɗannan sun yi daidai da( 10.1%, 36.5%) da (0.9%) bi da bi na jimlar ingantattun ƙuri'un da aka jefa. An zabi Boon a kan tikitin jam'iyyar Democratic Congress.[8][9]

Jam'iyyar National Democratic Congress ta samu kujeru( 7), na 'yan majalisa a zaben da aka yi a yankin Upper West na kasar Ghana.[10]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Boon Kirista ce.[2] Ta auri Jacob Bawiine Boon, lauyace kuma tsohuwan yar majalisa mai wakiltar mazabar Lambussie ce kuma tsohuwan shugaban gundumar Jirapa/Lambussie ce.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. Sam, Eben C. (12 March 2005). "The Mirror: Issue 2622 March 12 2005".
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 Ghana Parliamentary Register, 2004–2008. Ghana: The Office of Parliament. 2004. p. 247.
  3. 3.0 3.1 "MP for Lambussie sworn in". www.ghanaweb.com. 9 June 1999. Retrieved 21 May 2020.
  4. "All is set for the Lambussie bye-election". www.ghanaweb.com. 26 May 1999. Retrieved 21 May 2020.
  5. "Lambussie – Karni Constituency – Election 2016 Results". Peace Fm Online. Retrieved 21 May 2020.
  6. 6.0 6.1 FM, Peace. "Ghana Election 2000 Results - Lambussie - Karni Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-09-02.
  7. 7.0 7.1 FM, Peace. "Ghana Election 2000". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-09-02.
  8. 8.0 8.1 8.2 Elections 2004; Ghana's Parliamentary and Presidential Elections. Ghana: Electoral Commission of Ghana; Friedrich Ebert Stiftung. 2005. p. 189.
  9. 9.0 9.1 9.2 FM, Peace. "Ghana Election 2004 Results – Lambussie – Karni Constituency". Ghana Elections – Peace FM. Retrieved 3 August 2020.
  10. "Statistics of Presidential and Parliamentary Election Results". Fact Check Ghana (in Turanci). 1 August 2016. Retrieved 3 August 2020.