Ali Mohammed Ghedi
Ali Mohamed Gedi ( Somali , Larabci: علي محمد جيدي ) An haife shi a ranar 2 ga watan Oktoba,shekara ta alif 1952, wanda aka fi sani da Ali Gedi, kasance Firayim Minista na gwamnatin rikon kwarya ta Kasar Somaliya daga shekarar 2004 zuwa shekara ta 2007. Ba a san shi sosai ba a fagen siyasa lokacin da aka nada shi a matsayin firaminista a watan Nuwamban shekara ta 2004. Yana da alaƙa da ƙabilar Abgaal na Mogadishu ta dangin Hawiye, ɗaya daga cikin manyan iyalai huɗu na Kasar Somaliya. Da kyar ya kuma tsira daga harin kunar bakin wake da aka kai gidansa wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane bakwai a ranar 3 ga watan Yunin shekara ta 2007.[1][2][3]
Ali Mohammed Ghedi | |||
---|---|---|---|
23 Disamba 2004 - 30 Oktoba 2007 ← Abdi Yusuf hussein (en) - Salim Aliyow Ibrow (en) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Mogadishu, 2 Oktoba 1952 (72 shekaru) | ||
ƙasa | Somaliya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Mogadishu University (en) University of Pisa (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Employers | Somali National University (en) | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | Transitional Federal Government (en) |
Tarihin rayuwa
gyara sasheAn haifi Ali Mohamed Gedi a Mogadishu, Somalia a shekara ta 1952. Ya fito ne daga Abgaal daga cikin Hawiye.
Gedi ya tashi daga wurin mahaifiyarsa. Mahaifin Gedi ya kasance hafsan soja, kuma a shekara ta 1978 ya shiga hukumar tsaro ta farin kaya ta Kasar Somaliya (NSS) a karkashin mulkin Siad Barre a mukamin Kanar.
Gedi ya yi karatu a Jamal Abdul Nasser High School a garin Mogadishu, yana kammala karatu a shekara ta 1972. Ya kammala karatun soji da bautar kasa, sannan kuma ya koyar a farkon shekara ta 1970. A jami'a, Gedi yayi fice a karatun sa, sannan ya wuce zuwa jami'ar Pisa . Ya kammala karatunsa a shekara ta 1978, daga nan kuma sai Jami’ar Kasar Somaliya (Faculty of Veterinary Medicine) ta dauke shi aiki a matsayin mataimakin malami. Daga shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1983, ya yi karatu a Jami'ar Pisa don karatun digiri na biyu kuma ya sami Digiri na Doctorate a kan ilimin dabbobi da tiyata. Sannan ya koma koyarwa a shekara ta 1983 a matsayin malami kuma ya shugabanci sashen har zuwa shekara ta 1990.
Sulhun siyasa
gyara sasheYa halarci tarurrukan sasanta siyasa a: Mogadishu a shekara ta (1994 - 1996), a Alkahira, Misira a shekara ta (1997), a Addis Ababa, Habasha (farkon shekara ta 1998), a Nairobi, Kenya (ƙarshen shekara ta 1998), a Beledweyne, Hiiran - Somaliya (1999). (Ali Mohamed Gedi, raba tare da Abdirahman Gutale).
Gwamnatin rikon kwarya
gyara sasheGwamnati a gudun hijira
gyara sasheA matsayinsa na shugaban gwamnatin ta wucin gadi, Gedi ya yi alkawarin kafa gwamnatin da za ta kunshi kowa, da kokarin yin sulhu tsakanin shugabannin yakin na Mogadishu.
Bayan yunkurin kashe shi da akayi saidai ba ayai nasara ba, Gedi ya gudu zuwa Nairobi, Kenya . A watan Yulin shekara ta 2005, ya koma garin Jawhar, ɗayan garuruwan biyu (ɗayan kuwa shi ne Baidoa ) wanda ake amfani da shi a matsayin babban haɗin Somaliyan na ɗan lokaci.[ana buƙatar hujja]
Gwamnati a garin Baidoa
gyara sasheA watan Maris na shekara ta 2006, fada ya barke tsakanin shuwagabannin kungiyar kawancen sake dawo da zaman lafiya da yaki da ta'addanci (ARPCT) da kungiyar kotunan musulinci (ICU) game da ikon Mogadishu, wanda ya ta'azzara a watan Mayu. Rikicin ya zama sananne da Yakin Mogadishu na Biyu . Firayim Minista ya bukaci shugabannin yaki, wadanda hudu daga cikinsu membobin gwamnatin TFG ne, su daina fada da ICU, amma an yi biris da wannan umurnin a duk duniya don haka Ghedi ya kore su daga Majalisar. Wadannan sun hada da: Ministan Tsaro na kasa Mohamed Afrah Qanyare, Ministan Kasuwanci Musa Sudi Yalahow, Ministan kula da tsugunar da Mayakan Issa Botan Alin da Ministan Harkokin Addini Omar Muhamoud Finnish .
Komawa zuwa Mogadishu
gyara sasheA cikin watan Disambar 2006, ICU da mayaƙan sa kai masu kishin Islama sun sha kashi ainun daga sojojin TFG da na kasar Habasha, waɗanda a ranar 29 ga watan Disamba suka shiga Mogadishu ba tare da hamayya ba. Kodayake an yi wa Ghedi maraba da zuwa cikin garin, amma abokansa na Habasha sun fuskanci fusatattun mutane da suka jefi sojojin Habasha da duwatsu. [4]
A ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2007, ya ba da sanarwar "Zamanin shugaban yaƙi a Mogadishu yanzu ya ƙare." [5] Ayyukan Ghedi na farko sun hada da ayyana dokar ta- baci tsawon watanni uku, yana kira da a kwance damarar mayakan, tare da nada sabbin alkalai .
Murabus
gyara sasheGedi ya sanar da murabus dinsa a gaban majalisa a garin Baydhabo a ranar 29 ga watan Oktoban, shekara ta 2007, saboda sabanin da ke tsakaninsa da shugaban Somaliya, Abdullahi Yusuf . Ana rade-radin cewa Gedi ya yarda ya yi murabus saboda goyon bayan siyasa a nan gaba. [6] [7] Ya ci gaba da zama dan majalisa.
A farkon watan Janairun shekara ta 2008, Gedi ya ba da sanarwar cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a shekara ta 2009.
Political offices | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |
Manazarta
gyara sashe- ↑ Verhoeven, Harry (November 2018). Environmental Politics in the Middle East. ISBN 9780190916688.
- ↑ "Profile: Ali Mohamed Ghedi". BBC. 2004-11-04. Retrieved 2006-01-29.
- ↑ "Profile: Somali PM survives attack on home". ABC News. 2004-06-04. Archived from the original on 2008-04-20. Retrieved 2006-06-04.
- ↑ "Mixed signals in Mogadishu" The New York Times, 29 December 2006.
- ↑ Somali prime minister orders complete disarmament Associated Press
- ↑ "Somali prime minister resigns", Al Jazeera, October 29, 2007.
- ↑ "Somali prime minister steps down", BBC News, October 29, 2007.