Ali Fergani ( Larabci: علي فرقاني‎ (An haife shi a ranar 21 ga watan Satumbar 1952), manajan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Aljeriya. kuma tsohon ɗan wasa wanda ya taka leda a tsakiyar fili a matsayin ɗan wasan ƙwallon ƙafa.

Ali Fergani
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Aljeriya
Country for sport (en) Fassara Aljeriya
Sunan asali علي فرقاني
Suna Ali
Sunan dangi Fergani
Shekarun haihuwa 21 Satumba 1952
Wurin haihuwa Onnaing (en) Fassara
Harsuna Larabci
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football coach (en) Fassara
Matsayin daya buga/kware a ƙungiya Mai buga tsakiya
Mamba na ƙungiyar wasanni JS Kabylie (en) Fassara, NA Hussein Dey (en) Fassara da Kungiyar Kwallon Kafa ta Aljeriya
Wasa ƙwallon ƙafa
Participant in (en) Fassara 1982 FIFA World Cup (en) Fassara, 1980 Summer Olympics (en) Fassara, 1980 African Cup of Nations (en) Fassara, 1982 African Cup of Nations (en) Fassara da 1984 African Cup of Nations (en) Fassara
Ali Fergani da yan kungiyar sa

Sana'a gyara sashe

Fergani ya buga wa NA Hussein Dey da Jetizi-Ouzou ƙwallon ƙafa. Fergani ya buga wa tawagar ƙwallon ƙafar Aljeriya a gasar Olympics ta bazara a shekarar 1980. Ya kuma halarci gasar cin kofin duniya ta FIFA a 1982 a Spain. [1]

A shekarar 1981, Fergani ya zo na uku a fafatawar neman kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afrika .[2]

Bayan ya yi ritaya, an naɗa Fergani a matsayin mataimakin manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aljeriya, da kuma kocin tsohon kulob ɗin JS Kabylie. Aikinsa na gudanarwa ya fara da kyau yayin da ya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 1990 a ƙasarsa ta haihuwa.[3] An sake naɗa Fergani a matsayin kocin tawagar ƙasar Algeria a shekara ta 1995, amma bayan shekara daya aka kore shi, bayan da Kenya ta sha kashi.[4]

Bayan barin tawagar ƙasar, Fergani ya horar da ƙungiyoyin Tunisiya da dama, ciki har da Club Athletic Bizertin, Union Sportive Monastir da Stade Tunisien, da sauransu.

Bayan murabus ɗin Robert Waseige, an sake kiran Fergani ga tawagar ƙwallon ƙafa ta Algeria, a matsayin mai sarrafa.

A ranar 10 ga watan Oktoba, 2011, an nada Fergani a matsayin manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Algeria A.[5]


Manazarta gyara sashe

  1. Ali FerganiFIFA competition record
  2. Pierrend, Jose Luis. "African Player of the Year 1981". RSSSF. Retrieved 2009-07-11.
  3. "Ali Ferghani Biography and Statistics". Sports Reference. Archived from the original on 2020-04-18. Retrieved 2009-07-11.
  4. Mubarak, Hassanin. "Algeria National Team Coaches". RSSSF. Archived from the original on 3 June 2009. Retrieved 2009-07-11.
  5. EN A' : Ali Fergani nouveau sélectionneur Archived 2012-02-13 at the Wayback Machine; DZFoot.com, 10 October 2011.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

  • Ali Fergani at National-Football-Teams.com