Hajji (larabci) wasu lokutan akan furta Hadji, Haji, Alhaji, Al hage, Al hag ko El-Hajj) wani suna ne da ake radama musulmin da yaje kasar Saidi Arabiya ya yi akin Hajji (daya daga cikin shika shikan Musulunci biyar.[1] A wasu lokutan kuma akan kira wani muhimmin mutum da lakanin Alhaji koda kuwa bai je Makka ba. Sannan kuma a mafi yawan tsakankanin musulamai ana kiran wani da Alhaji ne domin a girmama shi. Ana saka Alhaji ne kafin sunan mutum, missali Alhaji Abubakar.

Infotaula d'esdevenimentAlhaji
Iri taken girmamawa
Suna saboda Aikin Hajji
Addini Musulunci
Mahajjata a hajjin 2010
Alhaji a yayin aikin hajji
Mabiya Addinin kirista

A KiristanciGyara

Ana amfani da kalmar "Hadži" a kirustancin asali ga mutumin da yaje ziyara Jerusalem anan ne ake kara kalmar a farkon sunan mutum, misali '"Hadži-Prodan

Asalin KalmarGyara

Asalin kalmar Alhaji tazo ne daga harshen larabci ḥājj, mai nuna aikatau da ma'anar ḥajja ("yin aikin hajji"). da mafurtar ḥajjī ta sami usuli daga kalmar Hajj da karin dafa goshi na harafini -ī, kuma Wannan ne yawanci wadanda ba Larabawa ba suke furtawa. A wasu wuraren taken yana zama kamar sunan iyali ne, misali, Hadžiosmanović (dan alhaji usman)

ManazartaGyara

  1. Malise Ruthven (1997). Islam: A very short introduction. Oxford University Press. p. 147. ISBN 978-0-19-285389-9.