Alf Lomas
Alfred Lomas, (30 ga watan Afrilu shekarar 1928 - 6 ga watan Janairu shekarar 2021) ɗan siyasan Biritaniya ne a karkashin jam'iyyar Labour wanda ya yi aiki a matsayin dan Majalisar Tarayyar Turai (MEP) mai wakiltar mazabar Arewa maso Gabashin London tun farkon kafa ta, a zaɓen Turai na farko a shekarar 1979 har zuwa lokacin da aka sake tsara mazabu a shekarar 1999.[1][2]
Alf Lomas | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
19 ga Yuli, 1994 - 19 ga Yuli, 1999 District: London North East (en) Election: 1994 European Parliament election (en)
25 ga Yuli, 1989 - 18 ga Yuli, 1994 District: London North East (en) Election: 1989 European Parliament election (en)
24 ga Yuli, 1984 - 24 ga Yuli, 1989 District: London North East (en) Election: 1984 European Parliament election (en)
17 ga Yuli, 1979 - 23 ga Yuli, 1984 District: London North East (en) Election: 1979 European Parliament election (en) | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Stockport (en) , 30 ga Afirilu, 1928 | ||||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||||
Harshen uwa | Turanci | ||||||||
Mutuwa | 6 ga Janairu, 2021 | ||||||||
Karatu | |||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Wurin aiki | Strasbourg da City of Brussels (en) | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Labour Party (en) |
Ilimi da Aiki
gyara sasheLomas ya yi karatu a Stockport, kafin ya zama magatakarda, mai wa jirgin kasa signa, sannan kuma yayi aiki soja na dan lokaci. Ya shiga jam’iyyar Labour kuma ya zama kansila, sannan ya zamo cikakken ma'aikaci. A zaben Majalisar Turai na shekarar 1979, an zabe shi a London North East, kuma daga shekara ta 1985 zuwa shekarar 1987, ya zama shugaban jam'iyyar Labour a Majalisar Turai.[3]
A tsakanin Majalisa, Alfred LOMAS ya kasance Mataimakin Shugaban Majalisa, Memba na Ofishin kuma Memba na Ƙungiyar Socialist kuma Memba na kungiyar Member of the Group of the Party of European Socialists.
Ya kasance shugaba kuma memba na wakilai akan huldodin kasashen Amurka ta tsakiya da kuma kungiyar Contadora.
A lokacin mulkinsa, Alfred Lomas ya kasance memba na kwamitin harkokin siyasa; Memba na kwamitin raya kasa da hadin gwiwa; Memba na kwamitin kula da kasafin kudi; Memba na kwamitin koke-koke, sannan memba na kwamitin kula da shari'a da 'yancin 'yan ƙasa.
Ya kasance memba na wakilai akan dangantaka da Latin - Amurka; Memba na wakilai don dangantaka da kasar Canada; Memba na Tawaga a Kwamitin Haɗin gwiwar Majalisar EU-Cyprus kuma Memba na Wakilin Kwamitin Haɗin gwiwar Majalisar EU da Malta.
Alfred Lomas ya kasance memba daga Majalisar Tarayyar Turai a Majalisar Haɗin kai don Yarjejeniyar tsakanin ƙasashen Afirka, Caribbea da Pacific da Ƙungiyar European Economic Community (ACP-EEC). [4]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ "Alfred Lomas". MEPs European Parliament. Retrieved 19 February 2021.
- ↑ "Obituary: Alf Lomas, former political secretary of London Co-operative Society". COOP News. Retrieved 19 February 2021.
- ↑ BBC-Vacher's Biographical Guide 1996. London: BBC Political Research Unit and Vacher's Publications. 1996. p. 6-20. ISBN 0951520857.
- ↑ Email to former members association 14 January 2021
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sasheParty political offices | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |