hoton alexender
Alexander Djiku
Rayuwa
Haihuwa Montpellier, 9 ga Augusta, 1994 (29 shekaru)
ƙasa Faransa
Ghana
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Stade Malherbe Caen (en) Fassara-
SC Bastia (en) Fassara2012-
SC Bastia (en) Fassara2014-2016
  RC Strasbourg (en) Fassara5 ga Yuli, 2019-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Nauyi 74 kg
Tsayi 182 cm

Alexander Kwabena Baidoo Djiku (an haife shi a ranar 9 ga watan Agusta shekara ta alif 1994) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga kulob ɗin Strasbourg na Ligue 1. An haife shi a Faransa, yana wakiltar tawagar kasar Ghana.[1]

Sana'a/Aiki gyara sashe

Djiku ya yi aiki a matsayin matashi a Bastia. Ya buga ma kungiyar wasa har zuwa shekarar 2014, inda aka kara masa girma zuwa babban kungiyar. Bayan ya shafe shekaru uku a kulob din, ya koma Caen. Djiku ya fara buga wasansa na farko a wasan Coupe de la Ligue da Évian a watan Disamba 2013.[2] [3]

A ranar 11 ga Yuli 2017, ya koma Stade Malherbe Caen ta Ligue 1 kan kwantiragin shekaru hudu. Strasbourg ne ta saye shi a lokacin rani na 2019.[4]

Ayyukan kasa gyara sashe

Djiku dan asalin Ghana ne da kuma Faransa. Ya yi karo da manyan ‘yan wasan Ghana a wasan sada zumunci da Mali ta doke su da ci 3-0 a ranar 9 ga Oktoba 2020.[5] Ya buga wa Ghana wasa na biyu da Qatar a ranar 12 ga Oktoba 2020 inda ya taka rawar gani. Wasan na uku na Djiku ya zo ne lokacin da sabon kocin Black Stars ya ba shi damar fara wasan da Zimbabwe a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya inda Ghana ta ci 3-1.[6] Ya kasance yana cikin tawagar Ghana a gasar cin kofin kasashen Afrika na 2021 a Kamaru.

Manazarta gyara sashe

  1. [[http://www.africa-football.com/2017/07/11/]] mercao-sm-caen-alexander-djiku-en-approche- senegal/
  2. Alexander Djiku:: Alexander Djiku:: Strasbourg". www.playmakerstats.com . Retrieved 8 August 2019.
  3. (in French) LFP
  4. ALEXANDER DJIKU REJOINT LE RACING". Archived from the original on 23 July 2019. Retrieved 23 July 2019.
  5. Ayamga, Emmanuel (2022-01-18). "Fatawu Issahaku starts as Milo names Ghana's starting line-up against Comoros". Pulse Ghana. Retrieved 2022-02-06.
  6. 2022 World Cup qualifiers: Ghana player ratings against Zimbabwe". Goal.com. Retrieved 12 October 2021

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

  • Alexander Djiku – French league stats at LFP – also available in French
  • Alexander Djiku at L'Équipe Football (in French)
  • Alexander Djiku at Soccerway