Alan Fitch
Ernest Alan Fitch (10 Maris 1915 - 7 Agusta 1985). ɗan siyasa ne ƙarƙashin Jam'iyyar Labour ta Biritaniya.
Karatu da Aiki
gyara sasheFitch ya sami ilimi a Makarantar Kingwood, Bath (1927-1932), kuma yayi aiki a Ma'aikatar ma'adinai. Ya wakilci ma'aikatan hakar ma'adinai a kwamitin zartarwa na Majalisar Labour na Lancashire da Cheshire.
Siyasa
gyara sasheZaɓe
gyara sasheAn zaɓe shi a majalissar dokoki na kasa a matsayin dan majalisa mai wakiltar Wigan a zaben fidda gwani na shekarar 1958, bayan mutuwar dan majalisar jam'iyyar Labour Ronald Williams. An sake zabe shi a babban zabuka bakwai masu zuwa, kafin ya sauka a babban zaben 1983, lokacin da Roger Stott ya rike matsayin daga jam'iyyar Labour.
Dan majalissa
gyara sasheFitch ya kasance ɗaya daga cikin 'yan majalisa biyu na Wigan a karni na 20 waɗanda suka ajiye aiki (ritaya) a maimakon su mutu a ofis. Magajinsa Roger Stott ya gaji matsayin kuma ya mutu a ofis a 1999.
Mataimaki
gyara sasheFitch ya kasance Mataimakin whip na majalisa daga 1964 zuwa 1966, Kwamishinan Baitulmali daga 1966 zuwa 1969 da Mataimakin Chamberlain na Gidan daga 1969 zuwa 1970, kuma ya kasance memba na kwamitin da aka zaba na masana'antu na kasa. Fitch ya kasance memba na Majalisar Tarayyar Turai.
Manazarta
gyara sashe- Times Guide to the House of Commons 1979
- Leigh Rayment's Historical List of MPs
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Hansard 1803–2005: contributions in Parliament by Alan Fitch
Unrecognised parameter | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |
Political offices | ||
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |