Al-Bakara (larabci| البقرة fassara Saniya) itace surah ta biyu kuma wacce take da mafi yawan ayoyi acikin Al-Qur'an.[1] Tana da yawan ayoyi guda 286, da kalmomi guda 6,201 da kuma yawan bakake guda 25,500.[2] Ita Surah Madaniyya, wato a garin Madina ne aka saukar da ita, bayan Hijira, banda wasu kadan daga cikin ayoyi daga ciki, wadanda aka saukar lokacin Hajjin Bankwana, wanda itace Hajjin Annabi Muhammad S.A.W.[3]

Al-Bakara
Surah
Bayanai
Bangare na Al Kur'ani
Suna a harshen gida البقرة
Suna a Kana めうし
Suna saboda Saniya
Akwai nau'insa ko fassara 2. The Cow (en) Fassara da Q31204645 Fassara
Harshen aiki ko suna Larabci
Full work available at URL (en) Fassara quran.com…
Has characteristic (en) Fassara Saurin Medina
Ayoyin farko na surah al-Baqarah

Itace surah mafi tsawo a Kur'ani. Itace Surah ta karshe da aka saukar a Madina, amma maban-bantan ayoyin an saukar dasu a wurare daban-daban, aya mai tsawo wanda take magana akan riba (cin kudin ruwa) kuma an saukar da ita ne a kusan karshen rayuwar Annabi Muhammad s.a.w, bayan bude garin Makkah (Maariful Quran).

Aya ta 281, acikin surar itace aya ta karshe da aka saukar acikin Alkur'ani, a 10 ga watan Dhul al Hijjah shekara ta 10 A.H., sanda Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana kan gudanar da aikin Hajjin sa na karshe, kuma bayan kwanaki 80 zuwa 90 sai ya rasu. (Kurtubi).

Surah al-Bakarah ta wajabtar da yin azumi akan musulmi lokacin watan Ramadan.[4]

Anazarci gyara sashe

  1. Salwa M. S. El - Awa, Introduction to Textual Relations in Qur'an, pg. 1. Part of the Routledge Studies in the Qur'an series. London: Routledge, 2005. ISBN|9781134227471
  2. Ibn Kathir
  3. Mahmoud Ayoub, The Qurʾan and its interpreters, pg. 55. Albany: State University of New York Press, 1984. ISBN|9780791495469
  4. Michael Binyon, Fighting is 'allowed' during the holy month of fasting The Times, 18 December 1998