Riba a Musulunci
Ma'anar Riba a yaran larabci: Ita ce kari da bunkasa, anacewa: Ribar dukiya shi ne idan ta karu kuma ta bunkansa, kuma ya karu sau hamsin. Ana anfani da Kalmar riba ga dukkanin cinikin da ya zama haramtacce. Riba a gun malaman fikhu: ita ce kari akan wasu abubuwa kebbantattu. Ko kuma Yarjejeniya ce akan wani abu kebantacce wanda ba'a sani ba a san yanayinsa ba a mahanga ta musulunci a lokacin da aka kulla yarjejeniyar, ko ma tare da jinkiri a abubuwan da za a karba biyu ko daya daga cikinsu.[1]
Hikimar Harumta Riba a Musulunci
gyara sashe1. Rashin samun daidaito tsakani wahala da anfanuwa domin kasance wan mai bashi kuma wanda ya ba da ribar, bai yi wani kokari ba, kuma bai yi wani aiki ba, sannan kuma ba ya daukar asara, na abinda ya auku na a kasuwancin ada kuma abinda ya mallaka na riba.[2] 2. Rugujewar tattalin arzikin al'umma, da sababin mai bashi zai dogara ne da riba saboda ha shi ba zai yi wani aiki ba, sa'annan ya sa shi ya zama mai yawan hutawa mai yawan kasala, don kodayin riba da kuma kuntatawa wanda aka ba bashi, saboda neman abinda zai cika ka'idojin riba. 3. Rugujewar kyakkyawar zamantakewa tsakanin al'umma ta sanadiyyar rashin taimako tsakanin mutane, na abunda zai tamaka dole wajan tarwatsa kan jama'ah da yaduwar kyashi da son kai, maimakon taimako da soyyaya da fifita mabukata tsakanin al'umma.[3] 4. Raba mutane zuwa mataki biyu masu jayyaya da juna, matakin masu neman wuce iyaka da masu nuna finkarfi da dukiyoyin su, da kuma matakin talakawa raunana wa.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://islamhouse.com/ha/books/2778721#t72
- ↑ https://islamqa.org/hanafi/askimam/4261/my-question-is-regarding-a-riba-mortgage-i-bought-a-house-in-my-country-by-riba-mortgage-2-years-ago-when-i-was-non-muslim-i-was-christian-then-so-i/
- ↑ https://www.soundvision.com/article/5-ways-to-deal-with-the-dilemma-of-riba