Akpanoluo Ikpong Ikpong Ette NNOM (23, Satumba 1929-17 Satumba, 2018) Farfesa ne a Najeriya kuma tsohon sakatare da kuma mataimakin shugaban Cibiyar Kimiyya ta Najeriya.[1]

Akpanoluo Ikpong Ikpong Ette
Rayuwa
Haihuwa Jahar Akwa Ibom, 23 Satumba 1929
ƙasa Najeriya
Mutuwa 17 Satumba 2018
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a physicist (en) Fassara da Malami
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

A cikin 1991, an zabe shi Shugaban Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Najeriya don ya gaji Farfesa Caleb Olaniyan.[2] A 2003, ya sami lambar yabo mafi girma na ilimi a Najeriya, lambar yabo ta National Order of Merit Award.[3]

Rayuwa da aiki

gyara sashe

An haifi Ette a garin Upenekang, kuma daga 1944 zuwa 1948 ya halarci makarantar horar da Hope Waddell, kafin ya karanci kimiyyar lissafi a Kwalejin Jami'a dake Ibadan a shekarar 1949, inda ya kammala karatunsa na BSc a shekarar 1954. Bayan ya koyar a cibiyar horar da Hope Waddell daga 1954 zuwa 1959, ya kammala karatun sa na PhD a Jami'ar Ibadan daga 1959 zuwa 1966 yayin da yake karantarwa a wannan jami'a. An nada shi Farfesa a shekarar 1972.[4]

Ette ya mutu a shekarar 2018.[4]


Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

gyara sashe
  1. "OBITUARY Professor Akpanoluo Ikpong Ikpong Ette, FNIP, FSAN, FAS, NNOM (23 September, 1929 - 17 September, 2018)" (PDF). Bulletin. University of Ibadan. 12 November 2018. Archived from the original (PDF) on 24 January 2023. Retrieved 9 December 2019.
  2. "Members of Council". Nigerian Academy of Science. Archived from the original on 7 July 2015. Retrieved 7 June 2015.
  3. "Two Academics Bag 2003 Merit Award". Business HighBeam. Archived from the original on 10 July 2015. Retrieved 9 June 2015.
  4. 4.0 4.1 "OBITUARY Professor Akpanoluo Ikpong Ikpong Ette, FNIP, FSAN, FAS, NNOM (23 September, 1929 - 17 September, 2018)" (PDF). Bulletin. University of Ibadan. 12 November 2018. Archived from the original (PDF) on 24 January 2023. Retrieved 9 December 2019.