Akanbi Oniyangi
Akanbi Mahmoud Oniyangi (yayi rayuwa daga 1930 zuwa 17 ga watan Janairu shekarar 2006) ɗan siyasan Najeriya ne kuma tsohon ministan kasuwanci da tsaro a lokacin jamhuriya ta biyu da aka soke. An haife shi a jihar Kwara kuma yayi karatu a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya kasance lauya kuma shugaban Al'umma kafin shiga siyasa . [1]
A lokacin da yake rike da matsayin Ministan Tsaro, ya yi kokarin inganta dangantakar Najeriya da makwabtanta. Kasar Chadi dai na tattaunawa da kasar Libya, kuma tana karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya, ita kuma Kamaru na fama da rikicin kan iyaka da Najeriya.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Akanbi Oniyangi Dies At 76," Daily Champion, January 18, 2006