Ahmed Hassan Musa
Ahmed Hassan Musa (ya mutu a shekarar 1979) ya kuma kasance ɗan tawayen Chadi ne wanda ya halarci kashin farko na Yaƙin Basasan Chadi . Ya kasance mai tsattsauran ra'ayin addinin Islama na kusa da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, shi ne shugaban kungiyar hadin kan yaran Chadi ( Union Générale des Fils du Tchad ko UGFT), jam'iyyar siyasa ta Islama da' yan Chadi da ke zaman bauta a Sudan suka kafa. Saboda amincewa da anti-Muslim manufofin da shugaba François Tombalbaye.
Ahmed Hassan Musa | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Cadi |
Mutuwa | Ati (en) , 1979 |
Karatu | |
Harsuna |
Larabci Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Musa ya taba yin zaman hijira a Sudan lokacin fashewar wata tarzoma a cikin Guéra Prefecture, a shekarar 1965 wanda hakan ya buɗe masa kofofin sabbin damammaki. A saboda wannan dalili ne ya kafa ƙungiya a ƙasarsa ta gudun hijira a ranar 7 ga Satumban shekarar 1965 mai suna Liberation, wadda ta kasance ƙungiya ta farko ta nuna ƙin jini ga Tombalbaye. Lokacin da Tombalbaye ya fadi a juyin mulkin na shekarata 1975, Musa a sauƙaƙe ya sasanta da sabuwar gwamnatin. Shekaru huɗu bayan haka, a cikin shekarar 1979, Hissène Habré ya kashe shi a Ati.
Manazarta
gyara sashe- Histoire du Tchad Archived 2013-12-12 at the Wayback Machine (a Faransanci)