Adeyemi Ikuforiji
Sabit Adeyemi Ikuforiji ( ⓘ ) ; an haife shi ranar 24 ga Agusta 1958) masanin tattalin arzikin Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda ya zama kakakin majalisar dokokin jihar Legas daga shekarar 2005 zuwa 2015.[1][2] An gurfanar da shi ne tare da tsohon mataimakinsa Oyebode Atoyebi a kan tuhume-tuhume 54 na karkatar da kuɗaɗen da suka kai Naira miliyan 333.8, daga bisani an wanke shi daga zargin.[3][4]
Adeyemi Ikuforiji | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jahar Legas, 24 ga Augusta, 1958 (66 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta |
Babeș-Bolyai University (en) Jami'ar jahar Lagos |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
adeyemiikuforiji.org |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Sabit Adeyemi Ikuforiji a ranar 24 ga watan Agustan 1958 a Epe, ƙaramar hukumar jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya. Ya halarci Makarantar Local Authority Central a Epe kafin ya wuce makarantar Epe Grammar inda ya sami takardar shedar Makarantar Yammacin Afirka a watan Yuli 1975.[5] Ya sami digiri na farko da na biyu a fannin tattalin arziki daga Jami'ar Babeș-Bolyai da Bucharest Academy of Economic Studies.[6] Daga baya ya samu digirin digirgir a fannin kasuwanci a jami’ar Legas a shekarar 1980.[7]
Siyasa
gyara sasheYa fara harkar siyasa a matsayin babban sakataren jam'iyyar Unity Party of Nigeria. A shekarar 2003, ya tsaya takarar kujerar mazaɓarsa, Epe Constituency I, aka zaɓe shi, dan majalisar dokokin jihar Legas.[8] A cikin watan Disamba 2005, an zaɓe shi a matsayin kakakin majalisa a ƙarƙashin jam'iyar Alliance for Democracy.[9] A ranar 4 ga watan Yunin 2007 aka sake zaɓen shi a karo na biyu a matsayin kakakin majalisa ta 6 bayan ya fito a matsayin wanda ya lashe zaɓen daga mazaɓarsa.[10]
Har wayau a ranar 4 ga watan Yunin 2011 an sake zaɓen shi a karo na uku a matsayin kakakin majalissar ta 7, wanda ya yi mulki har zuwa 3 ga watan Yuni 2015.[11]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Ikuforiji Re-elected Lagos Speaker, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ "I don't need any petition to impeach Fashola -Ikuforiji". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ "2015 Gov Race: I Want To Succeed Fashola, Says Ikuforiji - P.M. NEWS Nigeria". pmnewsnigeria.com. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ "Alleged money laundering: EFCC closes case against former Lagos Speaker, Ikuforiji" (in Turanci). 2021-03-17. Retrieved 2022-02-07.
- ↑ Leadership Newspaper (15 November 2014). "Lagos 2015: Ikufuriji, Hamzat, Ambode Battle To Clinch APC Ticket". Nigerian News from Leadership News. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ "THE DAY I GOT A SCHOLARSHIP, MY POOR DAD DANCED NAKED –HON. ADEYEMI IKUFORIJI". nigerianbestforum.com. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ "At 54, Lagos Speaker Ikuforiji Trudges On, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ "Ikuforiji Willing To Succeed Babtunde Fashola In 2015". naij.com. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ Bright Owusu. "Ikuforiji re-elected speaker as Lagos inaugurates 7th Assembly". Ghanamma.com. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ "Lagos 2015-why the next gov should be Ikuforiji". Tribune.com. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
- ↑ "Lagos state house of Assembly: Ikuforiji re-elected speaker". theinfostride.com. Retrieved 18 April 2015.