Adenike Osofisan
Adenike Osofisan (An haife ta ranar 11 ga watan Maris, 1950). Ta kasance farfesar kimiyyar na’ura mai kwakwalwa ce wacce ta gwanance ta kware a fannin tattara bayanai da kuma kula da ilimi. Ita ce mace ta farko ‘yar Nijeriya da ta fara samun ilimi mai zurfi har zuwa matakin digirin digirgir (PhD) a fannin kimiyyar kwamfuta, wacce ta fara taka wannan damar tun a 1989. A shekarar 2006, ta zama cikakkiyar Farfesa a jami’ar Ibadan, hakan ya kai ta ga zama mace ta farko a dukkanin nahiyar Afrika da ta fara zama Farfesar kimiyyar kwamfuta.[1]
Adenike Osofisan | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Osogbo, 11 ga Maris, 1950 (74 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Obafemi Awolowo Georgia Tech (en) Jami'ar Ibadan (1991 - 1993) Master of Business Administration (en) |
Thesis director | Adebayo Dada Akinde (en) |
Dalibin daktanci |
Bamidele Ayodeji Oluwade (en) Babatunde Opeoluwa Akinkunmi (en) |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da university teacher (en) |
Employers | Jami'ar Ibadan |
Tarihin Rayuwa da Karatu
gyara sasheAdenike Osofisan ta kammala karatun sakandarinta ne a Fiwasaiye Girls’ Grammar School, da ke Akure, da kuma Comprehensice High School, Ayetoro a 1968. A tsakanin 1971 da 1976, ta samu digirinta na farko a jami’ar Ile-Ife, ta samu tallafin karatu daga gwamnatin tarayya tun a wancan lokacin bisa kokarinta inda ta kammala jami’a cikin cin moriyar wannan tallafin. Daga baya ta zo ta wuce zuwa cibiyar ilmin kimiyya ta Georgia a 1978, ta samu digirinta na biyu ne a Information and Computer Science a shekarar 1979. Ta kuma yi digirinta na uku (PhD) kan darasin ‘Data Processing Model for a Multi-access Computer Communication Network’ wacce ta kammala a 1989 a jami’ar Obafemi Awolowo a karkashin sanya idon Adebayo Akinde. A 1993, ne ta kammala wani shiri na musamman a fannin iya gudanar da harkokin kasuwanci da ririta kudade a jami’ar Ibadan.[2]
Ayyuka
gyara sasheFarfesa Osifisan ta fara aikin koyarwa ne a kwalejin kimiyya ta Ibadan a shekarar 1979. Ta kwashe tsawon shekaru tana koyarwa a wannan kwalejin daga baya har ta zo ta zama shugabar tsangayar kimiyya na wannan kwalejin. A 1999 ne kuma ta fara aiki da jami’ar Ibadan, nan take ta fara aiki a matsayin mai rikon mukamin shugaban sashin kimiyya na jami’ar. A 2003, ta samu likafarta ya daukaka zuwa karamar farfesa, kama-kama ta samu zuwa ga matakin cikakkiyar Farfesa ne a shekarar 2006. Har-ila-yau, ta kasance malamar jami’ar da ke koyarwa na wucin gadi a jami’ar Legas.[3]
Kungiyoyi
gyara sasheAdenike Osofisan ta kasance mambar majalisar amintattu na Nigeria Internet Registration Association (NIRA); tsohowar mambar cibiyar ilimin lissafi ta kasa ‘Nigeria Mathematical Centre’ da Nigeria Institute of Management (NIM) Councils. Yanzu haka ita mambar majalisar ilimi ce; mambar Africa Academic Board of SAP (Systems, Applications, and Products in Data Processing). Sannan kuma, Adenike ita ce Darakta a makarantar nazarin ilimin kasuwanci ta ‘Ibadan School of Business’ (UISB). Ita ce mace ta farko da aka fara zama shugabar Nigeria Computer Society College of Fellows a watan Yulin 2017.[4]
Karramawa
gyara sasheTa amshi lambobin yabo da na shaida da dama a rayuwarta. Ta kuma yi wallafe-wallafe na littafai da mukalolin da a yanzu haka ake amfani da su a cibiyoyin ilimi da daman gaske.[5]
Manzarta
gyara sashe- ↑ https://hausa.leadership.ng/adenike-osofisan-mace-ta-farko-farfesar-kimiyyar-kwamfuta-a-nahiyar-afrika/
- ↑ https://tribuneonlineng.com/govt-should-play-less-politics-with-education-professor-osofisan/
- ↑ https://punchng.com/i-was-called-iron-lady-for-being-a-successful-woman-prof-osofisan/
- ↑ https://www.sunnewsonline.com/why-govt-needs-to-train-youths-in-ict-odusote/
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2022/02/osofisan-bags-global-golden-awards-as-most-notable-top-distinguished-senior-professor/