Fazal bin Muhammad bin Ali ( Larabci : فضل بن محمد بن علي,[1]; an haife shi 1016 - 1084) wanda aka fi sani da "Abu Ali Farmadi" ko kuma kawai "Abu Ali" waliyyi ne na sarkar zinare na Naqshbandi, kuma fitaccen Sufaye.[2] shugaba kuma mai wa'azi daga Ṭūs, Khorasan Iran . Ya shahara da zama malamin Al-Ghazali a lokacin kuruciyarsa.

Abu Ali Farmadi
Rayuwa
Haihuwa Tus (en) Fassara, 1016
Mutuwa Tus (en) Fassara, 1084
Malamai Ibn Tahir al-Baghdadi (en) Fassara
Baba Kuhi of Shiraz (en) Fassara
Abd al-Karīm ibn Hawāzin Qushayri (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a

Haihuwa gyara sashe

An haife shi a shekara ta 407 bayan hijira. Ana kiransa al-Fārmadī saboda wurin haihuwarsa, Farmad, ƙauye da ke kusa da Ṭūs. [3]

Ilimi gyara sashe

Bayan kammala karatunsa na firamare ya shiga madrasah na sanannen Sufi Abdulkarim Qushayri a Nishapur sannan ya kasance mai bin Abu Al-Hassan Al-Kharqani.[4] Ya kasance almajirin Imam Abu Qasim Qaisheri da Sheikh Abu Qasim Jurjani . cikin kwanakinsa na ƙarshe ya sami ni'imar ruhaniya daga Sheikh Abdul Hasan Qarqani.[5]

Tarihin Rayuwa gyara sashe

Ana kiran Abu ali Farmadi Masanin Mai rahama kuma Majibincin Soyayyar Ubangiji. Malamin mazhabar Shafi'iyya ne kuma 'arif na musamman (wanda aka baiwa ilimin ruhi). Ya shagaltu sosai a cikin Mazhabar Salaf (malaman karni na farko da na biyu bayan hijira) da na Khalaf (malamai na baya), amma ya yi tasiri a cikin Ilimin Tasawwuf. Daga cikinsa ya ciro wani ilmin sama wanda ya zo a cikin Alkur’ani dangane da al-Khidr salla: “Kuma Mun sanar da shi daga iliminmu na sama” [18:65].[6]

Mutuwa gyara sashe

Ya rasu a ranar 4 ga Rabi-ul-Awwal shekara ta 477 bayan hijira a ranar Alhamis.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

Nassoshi gyara sashe

  1. Kabbani, Muhammad Hisham (2003). Classical Islam and the Naqshbandi Sufi Tradition (in Turanci). ISCA. ISBN 978-1-930409-10-1.
  2. Hanif, N. (2002). Biographical Encyclopaedia of Sufis: Central Asia and Middle East (in Turanci). Sarup & Sons. ISBN 978-81-7625-266-9.
  3. al-Samʿānī, 10/124; Yāqūt, 3/839
  4. The Golden Chain of Transmission MASTERS Nagshibandi way Osman Nuri Topba§ © Erkam Publications 2016 / 1437 H Istanbul - 1437 / 2016 08033994793.ABA
  5. "Gulzar Auliya". 26 June 2019.
  6. "Abu Ali al-Farmadi | the Naqshbandi Haqqani Sufi Order of America: Sufism and Spirituality". naqshbandi.org. Archived from the original on 2019-03-31.