Abdul-Azeez Olajide Adediran
Abdul-Azeez Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor, ɗan siyasa ne a Najeriya, ɗan jarida, ɗan kasuwa, kuma masanin fasaha.[1] Shi ne shugaban kungiyar Lagos4Lagos kuma dan takarar gwamna a jihar Legas a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party tare da abokin takararsa, Funke Akindele.[2][3][4] Shine wanda ya karɓi lambar yabo ta 2021 Honorary Doctorate in Leadership and Governance daga Jami'ar Kudancin Amurka, Legas, Najeriya.[5]
Abdul-Azeez Olajide Adediran | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Kuruciya da ilimi
gyara sasheAn haifi Jandor ga dangin Alhaji Adeniran da marigayiya Mrs Ruth Oluwafunmilayo Adeniran a ranar 25 ga Nuwamba 1977 a Unguwar Mushin ta Jihar Legas. Jandor ya kammala karatun digiri ne a The Polytechnic Ibadan ; Jami'ar Modul, Vienna ; Makarantar Kasuwancin Jami'ar Howard, Washington DC, Amurka; da Jami'ar Oxford, Oxford, United Kingdom .
Aiki
gyara sasheJandor ya fara aikinsa a gidan jarida kuma ya kasance dan jarida fiye da shekaru ashirin. Daga karshe ya shiga siyasa a karkashin jam’iyyar APC.[6] Shi ne jagoran tafiyar Lagos4Lagos, motsi a karkashin APC. Daga karshe ya koma PDP kuma a halin yanzu shi ne dan takarar su na gwamna a zaben gwamnan Legas na 2023.[7]
Rayuwa
gyara sasheYana auren Maryam Olajide Adediran kuma suna da ‘ya’ya biyu; Fareedah Oluwamayokun Amoke da Fadhilulah Oluwamurewa Adedayo Akanniade Olajide-Adediran.[8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Olajide Adediran (Jandor): Biography, Wife, Children, Political Career, and Source of Wealth". NewswireNGR. 2022-07-13. Retrieved 2022-07-14.
- ↑ Jonathan, Oladayo (2022-07-13). "Lagos 2023: How Funke Akindele and I will defeat Sanwo-Olu, APC — PDP gov candidate - Premium Times Nigeria". Retrieved 2022-07-14.
- ↑ Informant247, The (2022-07-13). "Olajide Adediran Jandor Net Worth, Biography, Age, PDP, Wiki". The Informant247. Retrieved 2022-07-14.
- ↑ "Lagos4Lagos Visioner Jandor Wins PDP Guber Primary Election | Channels Television". www.channelstv.com. Retrieved 2022-07-14.
- ↑ "Abdul-Azeez Olajide Adediran Biography and Detailed Profile". Politicians Data. 2022-06-05. Retrieved 2022-07-14.
- ↑ "Olajide Adediran Jandor Biography, Net Worth, Age, Family, Wife". 2022-07-13. Retrieved 2022-07-14.
- ↑ Abdul-Azeez, Olajide Adeniran. "Official website"
- ↑ Abdul-Azeez, Olajide Adeniran. "Official website"