Malam Ɗanladi Sanusi-Maiyamba a lafazin magana shi ne Mai Tangale na 16 na masarautar Tangale.[1][2] Ya hau karagar mulki kwanaki 52 bayan rasuwar Dr. Abdu Buba Maisheru II, Mai Tangale na 15.[3] Gwamnan jihar Gombe ne ya naɗa shi bisa la’akari da dokar masarautar Gombe tare da tuntuɓar ‘yan majalisa.[4][5][6][7]

Ɗanladi Sanusi-Maiyamba
Emir (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Jihar Gombe, 1966 (57/58 shekaru)
Ƙabila Tangale (en) Fassara
Karatu
Harsuna Tangale (en) Fassara
Hausa
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Malam Ɗanladi Sanusi Maiyamba a ranar 12 ga Fabrairun shekarar 1966, a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar Gombe. Ya tafi makarantar firamare ta Billiri inda ya samu shaidar kammala karatunsa na firamare. Bayan haka, ya wuce makarantar jeka ka dawo, ta barikin sojoji da ke Yola inda ya samu shaidar kammala sakandare a shekarar 1984. Ya yi karatunsa na jami'a a Federal Polytechnic Bauchi inda ya yi digiri a fannin harkokin gwamnati.[3]

Ɗanladi Sanusi-Maiyamba ma'aikacin gwamnati ne wanda ya yi aiki a sassa da dama na gwamnati. Ya yi aiki a Ministry of Education Bauchi daga shekarar 1987 zuwa 1996.

Ya kasance a Kotun ɗaukaka ƙara ta Shari’a da ke Gombe a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2011 sannan ya bar aiki a Hukumar Ma’aikata ta Ƙaramar Hukumar daga shekarar 2011 zuwa 2016. A shekarar 2016 ya bar ƙaramar hukumar inda ya zama mai muƙami a ma’aikatar kiwon dabbobi da al’amuran makiyaya wanda ya kai har shekara ta 2018. A cikin wannan shekarar ne ya samu ganawa da Hukumar Hidima ta Majalisar Dokokin Jihar Gombe wadda ta kasance har zuwa ranar da ya hau karagar mulki.[3]

Manazarta

gyara sashe