Zeinat Sedki
Zeinat Sedki (4 ga Mayu, 1912 - 2 ga Maris, 1978) ƴar wasan kwaikwayo ce kuma 'yar wasan ban dariya ta ƙasar Masar.[1] Ta kasance ɗaya daga cikin mata masu fara wasan kwaikwayo a cikin fina-finai na Masar tare da Mary Mounib da Widad Hamdi.[2]
Zeinat Sedki | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Misra, 4 Mayu 1912 |
ƙasa | Misra |
Harshen uwa | Egyptian Arabic (en) |
Mutuwa | Kairo, 2 ga Maris, 1978 |
Karatu | |
Harsuna | Egyptian Arabic (en) |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm0781323 |
Tarihin rayuwa
gyara sasheAn haifi Zeinat Sedki Zeinab Mohamed Mosaad ranar 4 ga watan Mayu, 1912 a Alexandria, Misira. Ta auri wani mutumin da ya girme ta da shekaru 15 bayan mahaifinta ya tilasta mata barin makaranta. Ta sake aure bayan shekara guda. Bayan rasuwar mahaifinta, ta fara aikinta a matsayin ƴar rawa, kuma ta shiga ƙungiyar masu fasaha a farkon shekarun 1930. Ta gudu daga gida kuma ta shiga ƙungiyar wasan kwaikwayo ta wasan kwaikwayo da Naguib el-Rihani ya kafa inda ta yi wasan kwaikwayon shirin ya shahara, daga cikinsu akwai The Egyptian Pound (el Guineih el Masrî) a 1931. -Rihani ya ba ta sunan Zeinat Sedki maimakon sunan haihuwarta Zeinab Mohamed Saad.
Ta yi fim ɗinta na farko a fim ɗin 1934 na Mario Volpe The Accusation. Ta ba da gudummawar da ta samu ga fim ɗin "His Highness Wants to Marry" (1936). A cikin wannan fim ɗin, ta taka rawaa matsayin wata yarinya daga ƙauye. Daga baya za ta ci gaba da taka wanna rawar a kan a cikin wasan kwaikwayo na wasan kwaikwayo wanda Naguib el-Rihani da Badie Khairy suka rubuta. A ƙarshen aikinta, ta fara samun matsalolin kuɗi kuma ta fara sayar da kayan daki-(furniture) ɗinta don biyan kuɗin da ta kashe. A shekara ta 1976, tsohon shugaban ƙasar Masar Mohamed Anwar el-Sadat ya ba ta lambar yabo a The Art Feast kuma ya ba ta fansho na musamman.[3]
Fina-finai
gyara sashe- 1934 : Al-ittihâm [ The Accusation ], film by Mario Volpe.
- 1936 : Bisalamtouh ‘âwiz yitgawwiz [ Monsieur wants to get married ], film by Alexandre Farkache.
- 1944: Berlanti [ Berlanti ], film by Youssef Wahbi.
- 1949 : ’Ifrîtah hânim [ Madam the Devil ], film by Henry Barakat.
- 1950 : al-Batal [ The Hero ], film by Helmy Rafla.
- 1950 : al-Millionnaire [ The Millionaire ], film by Helmy Rafla.
- 1952 : The Sweetness of Love
- 1953 : Zalamounî al-habâyib [ Those I love have wronged me ], film by Helmy Rafla.
- 1953 : Maw’id ma’ al-hayâh [ Rendezvous with life ], film by Ezz El-Dine Zulficar.
- 1953 : Dahab, film d’Anwar Wagdi.
- 1954 : Qouloub al-nâs [ Human hearts ], film by Hassan al-Imam.
- 1954 : al-Ânissah Hanafi [ Miss Hanafi ], film by Fatin Abdel Wahab.
- 1954 : al Malâk al-zâlim [ The Unjust Angel ], film by Hassan al-Imam.
- 1954 : Innîh râhilah [ I'm leaving ], film by Ezz El-Dine Zulficar.
- 1955 : Madrasat al-banât [ The School for Girls ], film by Kamel el-Telmissany.
- 1956: Al-Qalb louh ahkâm [ The heart has its reasons ], film by Helmy Halim.
- 1957 : Ibn Hamido [ Hamido's son ], film by Fatin Abdel Wahab.
- 1958 : Châri’ al-houbb [ The Street of Love ] film by Ezz El-Dine Zulficar.
- 1960 : Hallâq al-sayyidât [ Hairdresser for ladies ], film by Fatin Abdel Wahab.
- 1962: Gamâeyat Qatl al-Zawgât al-Hazleya [The Comic Society for Killing Wives], film by Hasan El-Saifi.
- 1975 : Bint ismouhâ Mahmoud [ A girl called Mahmoud ], film de Niazi Mostafa.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ahmed, Lara (4 May 2019). "5 Reasons Zeinat Sedki Still Shines: Remembering Egypt's Queen of Comedy". Women of Egypt Magazine. Retrieved 30 September 2021.
- ↑ Essam, Angy (1 March 2019). "Six facts you need to know about Zeinat Sedky". Egypt Today. Retrieved 30 September 2021.
- ↑ Essam, Angy (1 March 2019). "Six facts you need to know about Zeinat Sedky". Egypt Today. Retrieved 30 September 2021.