Zanga-zangar Kawo Ƙarshen Zaluncin Gomnati

Zanga-zangar Ƙarshen rashin shuagabanci na gari wadda akayi mata maudu’i da #EndBadGovernance ko kuma #EndBadGovernanceInNigeria, jerin zanga-zangar da ake yi ta gama gari wadda jama’a suka fito a ko'ina a faɗin Najeriya[1] saboda tsadar rayuwa a ƙasar. Zanga-zangar ta yi ƙamari ne a ranar 1 ga watan Agustan 2024 lokacin da wata zanga-zangar lumana da akeyi ta rikiɗe zuwa tashin hankali bayan da hukumomin tsaron Najeriya suka yi yunƙurin dakile zanga-zangar.[2][3]

Zanga-zangar Kawo Ƙarshen Zaluncin Gomnati

Zanga-zangar da nufin kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari ta samo asali ne daga ƙara taɓarɓarewar tattalin arziki da yunwa da Najeriya ke fuskanta, wanda wakilin BBC, Simi Jolaoso, ya bayyana a matsayin "rikicin tattalin arziki mafi muni a cikin wannan zamanin", sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, musamman kan farashin abinci, wanda farashin komai ya nunnunka abinda ake saya #100 yanzu ya koma #600 ko kuma sama da haka ma. Wasu masana dai na alakanta rikicin da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, musamman cire tallafin man fetur da gomantin Tinubu tayi tun ranar da aka rantsar dashi kafin ma ya shiga ofos, da kuma faduwar darajar Naira biyo bayan cire turakarsa zuwa dalar Amurka, duk wannan a ƙarƙashin shugaba Bola Tinubu da aka tsara don kaɗai son rai irin na shugabannin Najeriya.[4] Mambobin gwamnati daban-daban, ciki har da shi kansa Tinubu, sun yi yunƙurin kawar ( hana zanga-zangar) da masu zanga-zangar, inda aka bayyana wasu matakai na tallafa wa matasa da kudi, wanda duka shaci-faɗi ce.[4] An fara zanga-zangar ne a ranar 29 ga Yuli, 2024 yayin da aka ga masu zanga-zangar a kan tituna suna nuna alluna masu dauke da sakonni kamar "Ya isa haka," "Dakatar da Manufofin cutar da ƴan ƙasa," "Mu ba Bayi ba ne a ƙasarmu," "Mu ba baza mu iya cigaba da jure wahalar da muke ciki ba," da " Dole ne a dawo da tallafin man fetur." [5] [6] [7] [8] A martanin da sojojin Najeriya suka mayar a ranar 29 ga watan Yulin 2024 sun toshe manyan hanyoyin da suka isa Abuja, babban birnin kasar. [9]

Manazarta

gyara sashe
  1. Ahmed, Abdulateef (2024-08-01). "#EndBadGovernance Protests Begin Across Nigerian Cities". News Central TV (in Turanci). Retrieved 2024-08-01.
  2. "#EndBadGovernance Protesters Gather At Abuja Stadium, Kick Off Demonstration Under Heavy Security". Sahara Reporters. Retrieved 2024-08-01.
  3. Mojeed, Abdulkareem (2024-08-01). "#EndBadGovernance: Protests turn violent in Kano, Gombe, Abuja". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-08-01.
  4. 4.0 4.1 Jolaoso, Simi. "Nigerians vow 'days of rage' over economic hardships". www.bbc.com. Retrieved 2024-08-02.
  5. Ogunrinde, Folashade (2024-07-28). "#EndBadGovernance Protest: Requesting location, organisers' identities constitutional - Police". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-07-29.
  6. Nigeria, News Agency of (2024-07-27). "FG tightens security at Nigerian borders ahead of #EndBadGovernance protest". Peoples Gazette Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-07-29.
  7. Rapheal (2024-07-28). "Nigerians divided over #EndBadGovernance protest". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-07-29.
  8. "Abuja Residents Shout 'We're Hungry' Amid Tinubu Minister, Wike's Plea To Shun #EndBadGovernance Protests | Sahara Reporters". saharareporters.com. Retrieved 2024-07-29.
  9. "Soldiers 'take over' major Abuja road 72 hours to hunger protest - Daily Trust". dailytrust.com/ (in Turanci). 2024-07-29. Retrieved 2024-07-29.