Zakari Ziblim
Zakari Ziblim ɗan siyasan Ghana ne kuma memba na majalisar dokoki ta farko a jamhuriya ta biyu ta Ghana mai wakiltar mazaɓar Nanumba a yankin Arewacin Ghana a ƙarƙashin membobin jam’iyyar Progress Party (PP).[1]
Zakari Ziblim | |||
---|---|---|---|
1 Oktoba 1969 - 13 ga Janairu, 1972 District: Nanumba District (en) Election: 1969 Ghanaian parliamentary election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 3 ga Afirilu, 1925 (99 shekaru) | ||
Karatu | |||
Makaranta | Training College (en) certificate (en) : koyarwa | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Malami da ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Zakari a ranar 3 ga Afrilun shekarar 1925 kuma ya zauna a Nanumba wani gari a tamale a Arewacin Ghana, Ya halarci Makarantar kwana ta Tamale da kuma Kwalejin Horar da Malamai ta Gwamnati . inda ya sami Takardar Horon Malamai daga baya kuma ya yi aiki a matsayin malami kafin ya shiga Majalisar.
Siyasa
gyara sasheYa fara siyasarsa a shekarar 1969 lokacin da ya zama ɗan takarar ɗan majalisa na wakiltar mazaɓar sa ta Nanumba a yankin Arewacin Ghana kafin a fara zaben majalisar dokokin kasar ta Ghana a shekarata 1969 .
An rantsar da shi a majalisar farko ta Jamhuriya ta Biyu ta Ghana a ranar 1 ga Oktoban shekarar 1969, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben kasar Ghana na shekarata 1969 da aka gudanar a ranar 26 ga watan Agusta 1969. Zamaninsa na dan majalisa ya kare ne a ranar 13 ga Janairun 1972.[2][3] [4]
Rayuwar mutum
gyara sasheZiblim musulmi ne.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Assembly, Ghana National (1970). Parliamentary Debates: Official Report (in Turanci). Ghana Publishing Corporation.
- ↑ The Legon Observer. Legon Society on National Affairs. 1969.
- ↑ Ghana Year Book (in Turanci). Daily Graphic. 1971.
- ↑ Chiefs and Politicians. Longman. 1979.