Zainab Usman Sa'idu Ɗakin Gari

Zainab Usman Sa'idu Ɗakin Gari ( Zainab Umaru Musa Ƴar'adua ) an haife ta ranar 1 ga watan Oktoba shekarar 1979, a Katsina, Najeriya. Ita ɗiya ce ga tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Umaru Musa Yar'Adua kuma matar tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Usman Sa'idu Nasamu Ɗakin gari.[1][2][3][4]

Zainab Usman Sa'idu Ɗakin Gari
Rayuwa
Haihuwa 1979 (44/45 shekaru)
Sana'a

Farkon Rayuwa da Ilimi gyara sashe

An kuma haifi Zainab a jihar Katsina a ranar 1 ga watan Oktoba, shekarar 1979. Ta fara neman ilimi ne a makarantar Firamare dake Katsina tsakanin shekarar 1986 zuwa 1992. Ta fara karatun sakandire ne a makarantar Mata ta Gwamnati dake Karamar hukumar [[Bakori]] tsakanin shekarar 1993 zuwa shekarar 1996, sannan ta kuma koma Essence International School Kaduna tsakanin shekarar 1996 zuwa 1999. Ta kasance ɗaliba a Jami’ar Maiduguri, Jihar Borno, daga shekara ta 2000 zuwa 2002. Tsakanin shekarar 2003 zuwa 2006, ta kasance ɗaliba a Jami'ar Huron, dake a London, United Kingdom sannan kuma Kwalejin Gudanar da Ayyuka.

Siyasa gyara sashe

Ta kuma kasance Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2015 sannan kuma ita ce wadda ta kirkira ZadaF Foundation for Women and Children Enpowerment.

Kyautuka/Girmamawa gyara sashe

  • CibiyarFederal Medical Center, Birnin Kebbi Child Health Week, Equity 2009 (5 August 2009)
  • Gidauniyar Women for Peace International Global Peace Diplomat (30 September 2009)

Littafan da ta wallafa gyara sashe

  • Kabir, Hajara Muhammad. Ci gaban matan Arewa . [Nijeriya].  . Saukewa: OCLC890820657.

Manazarta gyara sashe

  1. Kabir, Hajara Muhammad (2010). Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
  2. "Usman Saidu Nasamu Dakingari biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2022-05-16.
  3. siteadmin (2009-06-22). "Yar'adua's Family of Greed- A Photo Essay Of A Humble Beginning And Then A Super Luxurious Life". Sahara Reporters. Retrieved 2022-05-16.
  4. "Alleged Corruption: EFCC moves against Saraki's wife, Yar'Adua's daughter | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2015-07-22. Retrieved 2022-05-16.