Zainab Alwani
Zainab Alwani | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a |
Zainab Alwani yar fafutukar kare hakkin bil adama ne kuma kwararriya a Amurka. Ita ce shugabar kuma mataimakiyar farfesa a fannin ilimin addinin Islama a Makarantar Divinity na Jami'ar Howard .
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Zainab Alwani a birnin Bagadaza na kasar Iraki a shekara ta 1962 'ya ga Taha Jabir Alalwani ce . An kuma tilasta wa Alwani da danginta tserewa daga Iraki a lokacin tana shekara 7. Iyalansu suntafi Masar daga bisani Saudi Arabia. [1]
Alwani matashiya ce tayi karatu a jami'ar musulunci ta Imam Mohammad Ibn Saud . Ta samu digirin digirgir (PhD) a fannin shari'a ( Usulul Fiqh ) a jami'ar Islama ta kasa da kasa dake Malaysia . [2] Alwani kuma ita ce mace ta farko da ta fara zama malamar fiqhu a majalisar fiqhu ta Arewacin Amurka . [3]
Alwani mai fafutukar kare hakkin mata da yaran musulmai. Ta himmatu wajen ci gaba da tunanin mahaifinta da tsarin fiqhun tsiraru. Ta kware a fannin shari'a, karatun kur'ani, alakar musulunci da shari'a, da mata da iyali a musulunci . [4] Yar uwarta ita ce Malamar Musulunci Ruqaia Al-Alwani . Hadia Mubarak ta bayyana Zainab da Ruqaia a matsayin wani bangare na ci gaban mata musulmai masu tafsirin Alkur'ani.
Labarai
gyara sasheLittattafai
gyara sashe- Alusra fi Maqasid al sharia: Qira' fi Qadaya al zawaj waltalaq fi Amrika (The Objectives of Sharia and the family: Critical Reading in Marriage and Divorce in American Muslim Family) . Herndon, Virginia: Cibiyar Tunanin Musulunci ta Duniya (IIIT), 2013.
- Matan Musulmai Da ke kalubalanta a Duniya:Na neman Canji Ta Hanyar Rubutun Alqur'ani da Misalin Annabci . Cibiyar Nazarin Buri, 2012.
- Abin da Musulunci ya ce game da tashin hankalin cikin gida: Jagora don Taimakawa Iyalan Musulmi, 2008.
Labarai
gyara sashe- "Tare da Aisha a Zuciya: Karatun Suratul Nur ta hanyar haɗin kan tsarin Kur'ani a cikin Matan Musulmai da Adalci na Jinsi: Ra'ayoyi, Tushen, da Tarihi" editan Dina El Omari, Juliane Hammer, da Mouhanad Khorchide . Rana, 2020.
- "Kafāla: The Kur'ani-Prophetic Model of Care Marayu" a cikin Journal of Islamic Faith & Practice. 2020.
- "Koyarwar ta hanyan amfani da tafsirin : Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) a matsayin Malami kuma Murabbi" a cikin Mujallar Addinin Musulunci da Aiki, 2019.
- "Al-wahda al-bina'iyya li-l-Qur'an: A Methodology for Understanding the Qur'an in the Modern Day" in Journal of Islamic Faith and Practice, 2018.
- "Matan Musulmai a Matsayin Malaman Addini: Binciken Tarihi" a cikin Tauhidin Muslima: Muryar Mata Musulmai Masu Tauhidi Editan Ednan Aslan, Marcia Hermansen, da Elif Medeni. Peter Lang (Peter-Lang-Verlagsgruppe), 2013.
- "Tsarin Kur'ani don Haɗuwa cikin Dangantakar Iyali" a Canji Daga Ciki: Mabambantan Ra'ayoyi akan Rikicin Cikin Gida a cikin Al'ummar Musulmi wanda Maha Alkhateeb da Salma Elkadi Abugideirii suka shirya. Iyalai Masu Zaman Lafiya, 2007.
Nassoshi
gyara sashe