Yaren Ika (Nigeria)
Harshen Ika, yare ne na Igboid, wanda aka rarraba shi ƙarƙashin Igboid Nuclear a cikin dangin harshen Yeai.
Yaren Ika | |
---|---|
| |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-3 |
ikk |
Glottolog |
ikaa1238 [1] |
Yaren mutanen Ika ne na jihohin Delta da Edo na kudancin Najeriya amfani da yaren. [2]
Musamman ma, ’yan kabilar Ika suna yankin Arewa maso Yammacin Jihar Delta; amma wasu kamar Igbanke, Inyelen da Ekpon, yanzu haka suna jihar Edo. Al'ummar Ika galibi sun ƙunshi wadannan: Agbor, Owa, Umunede, Mbiri, Abavo, Orogodo, Otolokpo, Igbodo, Ute-Okpu, Ute-Ugbeje, Idumuesah Akumazi, Ekpon, Igbanke, Inyelen, Iru egbede (Jihar Edo). [2]
Sauran al’ummar Ika da aka samu a Jihar Edo sun hada da Owanikeke, Owa-Riuzo Idu, Igbogili, Ute Oheze, Owa Ute, Oheze Ute, Obagie N’Oheze, Oghada, da Ogan da Ute Obagie N’Oheze. A gidan rediyon Delta yanzu akwai labarai cikin yaren Ika. Ikas sun soma rubuta Littafi Mai Tsarki a yarensu, kuma an buga bisharar Markus, Luka, Matta da Yohanna a ,cikin Ika tare da wasu littattafai. Ifeanyi Okowa fitaccen dan Ika ne.
Ika kwatanta phonological
gyara sasheTakaitacce juxtasion na phonology tsakanin yarukan Ika guda uku daban-daban.
Turanci | Yaren Akumuzi (Arewa- Gabas) na Ika | Yaren Owa (Arewacin Kudu) na Ika | Yaren Agbor (Kudu) na Ika |
---|---|---|---|
'tufafi' | akwa | ekwa | ekwa |
'takarda' | akuwo | ekukwo | ehhwo |
' sandar tauna' | atu | etu | etu |
'soso' | elu | eru | eru |
'mai dadi' | mu | mu | uswo |
Karin bayani
gyara sashe
manazarta
gyara sashe- ↑ Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Yaren Ika". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
- ↑ 2.0 2.1 Empty citation (help)