Yannis N'Gakoutou
Yannis Clarence N'Gakoutou Yapéndé (an haife shi ranar 30 ga watan Satumba, 1998) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin winger na ƙungiyar Championnat National 2 Lyon La Duchère.
Yannis N'Gakoutou | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Cikakken suna | Yannis Clarence Ngakoutou Yapende | ||||||||||||||||||
Haihuwa | Saint-Denis (en) , 30 Satumba 1998 (26 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa |
Gabon Faransa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | ||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||
Ahali | Quentin Ngakoutou (en) | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | full-back (en) |
Farkon rayuwa
gyara sasheAn haife shi a Faransa, yana buga wa tawagar kasar Gabon wasa.
Aikin kulob/Ƙungiya
gyara sasheN'Gakoutou samfurin matasa ne na kulob ɗin Drancy da Monaco kafin ya fara babban aikinsa tare da ajiyar Monaco a 2016.[1] Ya koma GOAL FC a shekarar 2020, amma ya samu cikas da rauni. Daga nan ya koma Lyon La Duchère a ranar 25 ga watan Yunin 2021.[2]
Ayyukan kasa
gyara sasheAn haifi N'Gakoutou a Faransa mahaifinsa ɗan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da mahaifiyarsa 'yar Gabon.[3] Ya buga wasansa na farko na kasa da kasa tare da tawagar kasar Gabon a wasan sada zumunci da suka yi da Mauritania a ranar 4 ga watan Janairu 2022.[4] Ya kasance cikin tawagar Gabon da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2021.[5]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheN'Gakoutou ɗan'uwan ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Quentin N'Gakoutou.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "[Interview] Yannis N'Gakoutou: "Je veux m'imposer à l'AS Monaco". October 4, 2018.
- ↑ Jeanjean, Richard. "National | Le Monégasque Yannis N'gakoutou est duchérois"
- ↑ "Gabon: Yannis N'Gakoutou-Yapende va pouvoir jouer pour les Panthères". November 26, 2021.
- ↑ Strack-Zimmermann, Benjamin. "Mauritania vs. Gabon (1:1)". www.national-football-teams.com
- ↑ Oludare, Shina (18 December 2021). "Afcon 2021: Arsenal's Aubameyang, Brighton's Ella headline Gabon provisional squad". Goal
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Yannis N'Gakoutou at National-Football-Teams.com
- Yannis N'Gakoutou at Soccerway