Yaƙin Kanjaga yaƙi ne a Afirka wanda aka yi tsakanin Babatu da mutanen Kanjaga. An yi iƙirarin cewa an yi yaƙin ne a ranar 14 ga Maris 1897.[1] Hadin gwiwar Ameria da na Faransa sun ci Babatu da mayaƙansa.[2][3][4]

Infotaula d'esdevenimentYaƙin Kanjaga
Iri faɗa
Kwanan watan 14 ga Maris, 1897
Wuri Kanjaga (en) Fassara
Ƙasa Ghana
Participant (en) Fassara

Tarihi gyara sashe

Babatu da farko ya farma mutanen Kanjaga, ya ci su kuma ya dauki sarkinsu mai suna Amnu a matsayin kamammu. Babatu ya yi fada da wani abokin gaba wanda daga cikin sahu ake kira Ameria ko Hamaria. An kama Ameria daga garin Santejan ta Zabarma lokacin yana karami. Ameria wani lokacin yana samun nasara a yaƙe -yaƙe da tsohon maigidansa.[1] Ameria ya kira kansa 'Sarkin Gurunsi'.[2] An yi ikirarin cewa ya yi wa Babatu tawaye saboda mace.[4]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "Bulsa History – Buluk" (in Turanci). Retrieved 2020-08-16.
  2. 2.0 2.1 Kröger, Franz. "Raids and Refuge - The Bulsa in Babatu's Slave Wars". Research Review (Legon/Accra) (in Turanci).
  3. "Extracts from Bulsa History: Sandema Chiefs before Azantilow". www.buluk.de. Retrieved 2020-08-16.
  4. 4.0 4.1 "Extracts (1731-1910) of the "Chronology of Bulsa History" translated into English and supplied with some additions". www.ghana-materialien.de. Retrieved 2020-08-16.