Wilson Asinobi Ake
Wilson Asinobi Ake (an haife shi a ranar 21 ga watan Satumban shekarar 1955) tsohon ɗan majalisar dattawan Najeriya ne wanda ya wakilci yankin Rivers West daga shekarar 2007 zuwa 2015. Ɗan jam'iyyar PDP ne.[1]
Wilson Asinobi Ake | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Suna | Wilson |
Shekarun haihuwa | 21 Satumba 1955 |
Wurin haihuwa | Jihar rivers |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | mamba a majalisar dattijai ta Najeriya, mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar wakilai ta Najeriya, |
Ɗan bangaren siyasa | Rivers State People's Democratic Party (en) da Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAke ya sami digiri na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha, Fatakwal, Jihar Ribas.
Sana'ar siyasa
gyara sasheYa kasance mataimakin shugaban tsohuwar ƙaramar hukumar Ahoada daga shekarar 1990 zuwa 1991), kuma daraktan gidan talabijin na jihar Ribas daga shekara ta 1992 zuwa 1993. An zaɓe shi ɗan majalisar wakilai daga 1999 zuwa 2003.[1]
Bayan ya hau kan kujerar sa a majalisar dattawa, sai aka naɗa shi shugaban kwamitin aiyuka, ma’aikata da samar da ayyuka, sannan kuma memba na kwamitocin kula da wutar lantarki, ruwa, da ilimi.[1] A cikin tantancewar tsakiyar wa’adi da Sanatoci suka yi a cikin watan Mayun shekarata 2009, Thisday ya ce ya ɗauki nauyin ƙudirin gyara hukumar kula da ayyukan yi ta ƙasa, da kare ƴan wasa da mata na Najeriya da kuma haramta tallace-tallacen ƙarya kan ayyukan yi, shiga da kuma damar kwangiloli. Ya ɗauki nauyin wani ƙudiri na samar da guraben ayyukan yi da kuma dakatar da yin hijira ba bisa ƙa’ida ba, kuma ya haɗa hannu da wani ƙudiri na gurfanar da waɗanda ke da hannu a cikin saga na Halliburton.[2]
Wilson Ake ya sake zama ɗan takarar PDP na Sanatan Rivers West a zaɓen shekarata 2011. Ya samu ƙuri’u 34,931, inda ya ke gaban wanda ya zo na biyu daga jam’iyyar ACN da ƙuri’u 6,446.[3]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheAke yana da aure kuma yana da ɗa 1