Wihioka Chidi Frank ɗan siyasan Najeriya ne. Ya kasance memba mai wakiltar mazaɓar Ikwerre/Emuoha na tarayya a majalisar wakilai. [1] [2]

Wihioka Chidi Frank
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

ga Yuni, 2015 - ga Yuni, 2019
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwar farko

gyara sashe

An haifi Wihioka Chidi Frank a shekarar 1959 kuma ya fito daga Elele, ƙaramar hukumar Ikwerre, jihar Rivers. Ya kammala makarantar firamare a shekarar 1973 daga makarantar firamare ta jihar 3, Elele. Ya kammala karatu a shekarar 1978 daga County Grammar School, Ikwerre/Etche. Ya halarci Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas (RSUST) don samun Difloma ta Ƙasa a fannin Kimiyyar Dabbobi, a Jami'ar Calabar don karatun digiri na biyu. [1] [2]

Aikin siyasa

gyara sashe

Kafin ya zama ɗan Majalisar Wakilai a shekarar 2015, ya yi ayyuka da dama da suka haɗa da Shugaban Hukumar Kula da Gyaran Titin Jihar Ribas, Janar Manaja, Risopalm Oil Estate, da Kwamishinan Hukumar INEC. A shekarar 2022, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressive Congress (APC) zuwa Social Democratic Party (SDP). [3] [4]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-25. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. 2.0 2.1 Nation, The (2017-01-13). "Adedibu once wrote me a letter in RED ink -Ex-Oyo Resident Electoral Commissioner". The Nation Newspaper (in Turanci). Retrieved 2024-12-25. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  3. "Ex-Rivers Rep Wihioka dumps APC, blames Amaechi" (in Turanci). Retrieved 2024-12-25.
  4. towncrierng (2021-11-08). ""POPULAR CANDIDATE SHOULD BE ON BALLOT NOT SOMEONE WHO DOESN'T KNOW WHO'S WHO IN APC AND POLITICS OF RIVERS STATE" - ELDER CHIDI FRANK WIHIOKA REVEALS". Towncrier (in Turanci). Retrieved 2024-12-25.