Victor Ngumah
Victor Ngumah ɗan siyasan Nijeriya ne, ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a. Shi ne babban jami'in gudanarwa na kafar yada labarai ta Lumen. Ya lashe lambar yabo ta Mujallar Jama'a ta shekarar 2018 mai suna Media / Showbiz Personality da lambar yabo ta a shekarar da ta gabata shekara ta 2019 Peace Achievers for Peace Builder / Award for Excellence a fannin aikin taimakon al'umma da kuma sanin makamar jagoranci.
Victor Ngumah | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan kasuwa |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheNgumah dan asalin garin Ezinihitte Mbaise ne, jihar Imo, Najeriya . Ya yi karatun sa a makarantar firamare ta Mater Ecclesiae, Mbaise, jihar Imo. Bayan karatun sakandaren sa sannan ya zarce zuwa jami'ar Radford University Ghana inda ya sami digiri a Fasahar Sadarwar Zamani (ICT).
Aiki
gyara sasheNgumah ɗan siyasa ne a Najeriya ne, ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a. Shi ne babban jami'in gudanarwa na kafar yada labarai ta Lumen. A shekarar 2019, ya tsaya takara a babban zaben Najeriya na 2019 don wakiltar mazabar jihar Ezinihitte Mbaise a majalisar dokokin jihar Imo a karkashin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), bayan zaben, ya yi kira da a gyara dokar zaben Najeriya. . A ranar 10 ga watan Yulin shekarar 2019, an sanar da shi a matsayin darakta na SBOC Energy Services.
Ayyukan Bada Agaji
gyara sasheNgumah ya kafa Victor for Victory Global Foundation (VVGF) don haɓaka ƙwarewar matasa da kuma kula da marasa galihu. A shekarar 2018, ya kaddamar da "Operation Get Your Sight Back", inda ya rarraba tabarau masu ƙara ƙarfin gani ga mutanen da suke da nakasar ido.
Lambobin Yabo
gyara sasheShekara | Taron | Kyauta | Sakamakon | Ref |
---|---|---|---|---|
2020 | Kyautar Sarautar Afirka | style="background: #99FF99; color: black; vertical-align: middle; text-align: center; " class="yes table-yes2"|Lashewa | ||
2019 | Samun zaman lafiya | style="background: #99FF99; color: black; vertical-align: middle; text-align: center; " class="yes table-yes2"|Lashewa | ||
2018 | Mujallar Jama'a ta gari | style="background: #99FF99; color: black; vertical-align: middle; text-align: center; " class="yes table-yes2"|Lashewa |
Manazarta
gyara sashe