Venice Kamel Gouda farfesa ce a fannin bincike ta ƙasar Masar kuma tsohuwar ƙaramar ministar bincike ta kimiya daga shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da uku zuwa da casa'in da bakwai (1993-97).[1]

Venice Kamel Gouda
Rayuwa
Haihuwa 7 Oktoba 1934 (89 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Karatu
Makaranta Cairo University (en) Fassara
Ain Shams University (en) Fassara
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Malami da minista

Rayuwar farko gyara sashe

'Ya ce ga akawunta Kamel Gouda da matarsa Victoria Attalah, Venice an haife ta a ranar bakwai 7 ga watan Oktoba, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da talatin da huɗu 1934 kuma ta karɓi B.Sc. Ta yi Digiri a Jami'ar Ain Shams a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin da shida 1956. Ta yi M.Sc. a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin da tara (1959) da PhD a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da biyu (1962) daga Jami'ar Alkahira.[1]

Aiki gyara sashe

Gouda ta fara aikinta a matsayin mataimakiyar masaniyar kimiyyar sinadarai a Cibiyar Bincike ta Ƙasa (NRC) a cikin shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin da shida 1956 kuma daga shekarun alif dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da biyu 1962 zuwa dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da shida 1966, mataimakiyar farfesa ce a Kwalejin Fasaha ta Clarkson. A shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da ɗaya 1991, ta zama darektar NRC's apply inorganic chemistry division. A cikin watan Oktoba, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da uku 1993 Shugaban Masar Hosni Mubarak ya naɗa ta ministar bincike na kimiyya, muƙamin da ta rike har zuwa watan Yuli, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da bakwai 1997.[2]

Gouda mamba ce mai himma a Majalisar Dinkin Duniya ta corrosion kuma ta jagoranci tawagogin Masar da dama zuwa ƙasashen ketare. Dangane da gudunmawar da ta bayar ga binciken kimiyya, Cibiyar Nazarin Kimiyya da Fasaha ta Masar ta karrama ta a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da huɗu 1974. Hakanan an ba ta lambar yabo ta NRC da kayan ado na shugaban ƙasa na shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da shida (1976).[1]

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

  • Venice Kamel Gouda publications indexed by Google Scholar
  • Publications by Venice Kamel Gouda at ResearchGate

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 Publitec Publications (1 January 2007). Who's Who in the Arab World 2007-2008. Gruyter. pp. 338–39. ISBN 978-3-11-093004-7.
  2. "Speaker Details: Dr. Venice Kamel Gouda". Bibliotheca Alexandrina. Retrieved 9 November 2017.