Ummu Hakim
Ummu Ḥakīm bint al-Ḥārith ibn Hishām (larabci: أم حكيم بنت الحارث إبن هشام) Sahabiya ce, wacce ta kasance daya daga cikin sahabban Annabi Muhammad S.A.W, tana fita yaki tare da Sahabbai har aka kashe ta a Yakin Yarmuk.
Ummu Hakim | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Makkah, |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Al-Harith ibn Hisham ibn al-Mughira |
Mahaifiya | Fatima Bint Al-Waleed |
Abokiyar zama |
Ikrimata ibn Abi Jahl Khalid ibn Sa'id |
Ahali | Abd al-Rahman ibn al-Harith ibn Hisham (en) |
Sana'a | |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Rayuwa
gyara sasheUmmu Hakim diyar al-Harith al-Makhzumi ( ibn Hisham bn al-Mughira bn abd Allah bn Umar bn Makhzum)[1][2][3][4]. Sunan mahaifiyarta Fatima bint al-Walid bn al-Mughira bn Abd Allah bn Umar bn Makhzum.[5]
iIta ce matar Ikrima bn Abi Jahal,[2][6] wanda aka kashe a yakin Yarmuk.
A wata majiya kuma ta ce an auri Abu Sa’id Khalid bn Sa’id ne a yammacin da ya gabata kafin yakin Marj al-Safar, an kashe Abu Sa’id a yakin[3].
Daga baya kuma ta auri Umar bn al-Khattab[7] daga gare ta ta haifi ‘ya mace mai suna Fatima[4].
Yakin Uhudu
gyara sasheA yakin Uhudu ta raka Ikrima da sauran Kuraishawa na Makka wadanda suka yaki musulmi. Ita da wasu mata sun bugi ganguna yayin da suke jagorantar tawagar matan kuraishawa zuwa fagen fama.[8]
Yakin Makkah
gyara sasheA shekara ta 630 miladiyya lokacin da musulmi suka ci Makkah, Ummu Hakim ta musulunta tare da sauran kuraishawa[2][6][8]. Daga baya Ummu Hakim ta shawo kan mijinta Ikrima ya karbi Musulunci.[9]
Yakin Marj al-Saffar
gyara sasheBayan an kashe Abu Sa’id, Ummu Hakim ta kashe sojojin Rumawa guda bakwai da hannu guda da sandar tanti kusa da wata gada wadda a yanzu ake kiranta da gadar Umm Hakim kusa da Damascus[10] a lokacin yakin Marj al-Saffar a shekara ta 634.[11]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Faizer, Rizwi (5 September 2013). The Life of Muhammad: Al-Waqidi's Kitab al-Maghazi - Google Books. Routledge. ISBN 9781136921131. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Nuʻmānī, Shiblī (2003). Sirat Un Nabi the Life of the Prophet - Google Books. Adam Publishers & Distributors. ISBN 9788174351388. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ 3.0 3.1 Balādhurī, Aḥmad ibn Yaḥyá (2002). The Origins of the Islamic State: Being a Translation from the Arabic ... - Abu Al-Abbas Ahmad Bin Jab Al-Baladhuri, Aḥmad ibn Yaḥyá Balādhurī - Google Books. Gorgias Press. p. 182. ISBN 9781931956635. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ 4.0 4.1 ?Abar?; Tabari (1994-02-17). The History of al-Tabari Vol. 14: The Conquest of Iran A.D. 641-643/A.H. 21-23 - Ṭabarī - Google Books. State University of New York Press. ISBN 9780791412947. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ "Page 248 - Kitab al-Tabaqat al-Kubra ta al-Khanji - Fatima - al-Maktaba al-Shamela". shamela.ws (in Arabic). Archived from the original on 13 September 2021. Retrieved 2021-09-18.
- ↑ 6.0 6.1 Islamkotob. Companions of the Prophet - IslamKotob - Google Books. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ Nomani, Shibli (2003). LIFE OF OMAR THE GREAT, THE (AL-FAROOQ) - Shibli Nomani - Google Books. Adam Publishers & Distributors. ISBN 9788174353382. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ 8.0 8.1 Khan, Maulana Wahiduddin; k̲h̲Ān̲, Vaḥīduddīn (1992). God-oriented Life: In the Light of Sayings and Deeds of the Prophet Muhammad ... - Google Books. Goodword. ISBN 9788185063973. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ G̲h̲az̤anfar, Mahmūd Aḥmad (2009). Great Women of Islam: Who Were Given the Good News of Paradise - Mahmood Ahmad Ghadanfar - Google Books. Darussalam. ISBN 9789960897271. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ Engineer, Asgharali (2005). The Qurʼan, Women, and Modern Society - Asgharali Engineer - Google Books. Sterling Publishers Pvt. ISBN 9781932705423. Retrieved 2014-01-18.
- ↑ Ahmed, Leila (28 July 1993). Women and Gender in Islam: Historical Roots of a Modern Debate - Leila Ahmed - Google Books. Yale University Press. ISBN 0300055838. Retrieved 2014-01-18.