Udi Hills
Dutsen Udi, ko Dutsen Ugwueme da Udi, yana cikin ƙaramar hukumar Arewa ta jihar Enugu, Najeriya. Waɗannan tsaunuka sun haura daruruwan mita sama da matakin teku.[1]
Udi Hills | |
---|---|
General information | |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 7°10′00″N 7°30′00″E / 7.16667°N 7.5°E |
Kasa | Najeriya |
Tarihi
gyara sasheA cikin shekarar 1908, tudun Udi sun ja hankalin tawagar Birtaniya daga Akwa zuwa Middle Belt,[2] kuma a cikin shekarar 1909, 'yan mulkin mallaka na Birtaniya zuwa Najeriya sun aika da tawagar injiniyoyin ma'adinai zuwa Enugu don neman azurfa. Sai, suka sauka a Ngwo a saman tsaunin Milliken bayan sun gano kwal. [3] A kan gangara zuwa kudu sun kafa wani matsuguni ga ma'aikatan Afirka da aka sani da Alfred Camp ko Ugwu Alfred.[4] A shekarar 1915, tudun Udi shine wurin da aka fara bude ma'adinan kwal na farko a Najeriya amma babayanhekaru biyu aka rufe aka maye gurbinsu da ma'adinin Iva Valley.[5]
Tsarin ruwan sama a Udi Hills
gyara sasheLokacin damina na shekara yana ɗaukar watanni 9.7, daga 12 ga watan Fabrairu zuwa ranar 2 ga watan Disamba, tare da zazzagewar ruwan sama na kwanaki 31 na akalla inci 0.5. Watan da aka fi yawan ruwan sama a Udi shine a watan Satumba, tare da matsakaicin ruwan sama na inci 9.4.
Lokacin rashin ruwan sama na shekara yana ɗaukar watanni 2.3, daga 2 ga watan Disamba zuwa 12 ga watan Fabrairu. Watan da mafi ƙarancin ruwan sama a Udi shine a watan Janairu, tare da matsakaicin ruwan sama na 0.2 inci.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Enugu: Top 10 Tourist Attractions Every Nigerian Should Visit In The Coal City - Nigerian Bulletin - Naija Trending News". nigerianbulletin.com. Retrieved 2019-06-03.
- ↑ "EMC3 | Udi Hills". emc3nigeria.com. Retrieved 2019-06-03.
- ↑ "Udi-Nsukka Plateau | plateau, Nigeria". Britannica.com. Retrieved 2019-06-03.
- ↑ "content/ugwueme-and-udi-hills#". zodml.org. Retrieved 2019-06-03.
- ↑ "Udi Hills". Afro Tourism. Retrieved 2019-06-03.