Ubiaja, gari ne a karamar hukumar Esan Kudu-maso-Gabas ( LGA ), Jihar Edo, Najeriya. Garin na da da tsayin 221 m. Yawancin mutanen yankin sun fito ne daga ƙabilar Esan, ɗaya daga cikin manyan ƙabilun jihar Edo..[1]

Ubiaja

Wuri
Map
 6°40′N 6°23′E / 6.66°N 6.38°E / 6.66; 6.38
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajahar Edo
Ƙananan hukumumin a NijeriyaEsan ta Kudu maso Gabas
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
kasuwar ubiaja


Garin Ubiaja

Ba a san ainafin ranar da aka kafa Garin Ubiaja ba, amma an kafa masarautar da ta kasance babban birnin kasar a shekara ta 1463 da wasu bakin haure daga Daular Benin. An ce wani mutumi mai suna Edikholor, ma'ajin masarautar Bini ne ya kafa garin a zamanin mulkin Ewuare mai girma. Sunan kuma na iya zama nau'in "Obiaza", ma'ana ma'aji, ko kuma yana iya fitowa daga "Obize", nau'in kifin da ya taimaka wa Edikholor ketare rafi, kifi wanda har yanzu mutanen Ubiaja ba su ci ba.[2]

Ruwan sama

gyara sashe
 
Cikin garin Ubiaja

Garin Ubiaja yana cikin yankin da ake ruwan sama sosai, yana da kimanin 1,800 millimetres (71 in) zuwa 2,000 millimetres (79 in) na adadin ruwan sama a kowace shekara.

 
Wasu daga cikin abubuwan da ake nomawa a Ubiaja

Yanayin Ƙasar wajen ja ce kuma da yawa daga cikin mutanen yankin suna noma amfanin gona irin su doya, rogo da wake, ko kuma kayan amfanin gona da suka haɗa da dabino mai, koko da roba.

  1. Kings Polytechnic makaranta mai zaman kanta a garin.

Geography

gyara sashe

Al'umomin Ubiaja dake cikin karamar hukumar Esan Kudu-maso-Gabas, Jihar Edo, sun kunshi;

  • "Okuesan"
  • "Emu"
  • "Emunokhua"
  • "Ikeken"
  • "Ebhohimi" da
  • "Okhuodua".

Waɗanda su ne al’ummomin da suka haɗu suka samar da Esan ta Kudu maso Gabas a Ubiaja.

Manazarta

gyara sashe
  1. "WELCOME TO UBIAJA". Ubiaja Union. Archived from the original on 2009-09-05. Retrieved 2009-11-27.
  2. "Ubiaja newsletter". Ubiaja Union. Archived from the original on 2009-09-08. Retrieved 2009-11-27.