Fatima Isa Muhammad wacce aka fi sani da Teemah Yola ta kasance jaruma ce a masana'antar shirya fina-finai na Hausa wato Kannywood da ke arewacin Najeriya.[1] jarumar ta yi suna sanadiyyar wani fim mai dogon zango, mai suna labarina.

Farkon rayuwa

gyara sashe

An haifi Fatima a watan mayu 11 ga watan a shekarar 1993 a cikin garin Yola jihar Adamawa Nijeriya. Mahaifin ta shi yasata a makarantar firamare, bayan ta gama sakandiri ta sami shiga Jami'ar Maiduguri inda ta karanci harshen larabci.[2]

Sana'ar fim

gyara sashe

Ta fara fitowa a wasan kwaikwayo tun a shekarar 2015 wanda yafi fito da ita shine fim din labarina Mai dogon zango

Fina-finai

gyara sashe

Ta yi fina finai da dama, amman an santa a fim wanda fim din 'labarina', wani fim da Aminu Saira ke bayar da Umarni.[3]

Ga wasu fina-finai;[4]

  1. Labarina
  2. Ukku sau ukku
  3. Dakin Amarya
  4. Ragon Azanci
  5. Gida ukku
  6. Tozarci. da sauransu

Rayuwar sirri

gyara sashe

Fatima tayi aure inda ta haifi yara guda biyu, [ana buƙatar hujja] daga Nan ta rabu da mijinta ta shiga harkar fim gadan-gadan.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.bbc.com/hausa/media-57919897
  2. https://www.thefamousnaija.com/2020/09/fatima-teema-yola-biography-age-husband_4.html
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-11. Retrieved 2023-07-11.
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-11. Retrieved 2023-07-11.