Tarila Thompson
Tarila Emmanuel Thompson (an haife shi a watan Fabrairu 14, 1968) ɗan wasan kwaikwayon Najeriya ne, darekta, mai shirya fina-finai, marubuci kuma mawaƙi. Thompson ya fara aikinsa a shekara ta 1992 kuma ana yaba masa saboda rawar da ya taka wajen fara harkar fina-finai masu magana da Turanci a Najeriya da aka fi sani da Nollywood.
Tarila Thompson | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Tarila Emmanuel Thompson |
Haihuwa | Lagos,, 14 ga Faburairu, 1968 (56 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, filmmaker (en) da mawaƙi |
IMDb | nm2141940 |
An san Thompson don Love without Language (1993), Die Another Day (2004), Passion and Pain (2004) da Church Business (2006). Bayan ya dauki huta daga yin fim, Thompson ya dawo a shekar 2012 don yin fim ɗinsa na baya-bayan nan In the Creek, fim ɗin da aka yiwa lakabi da mafi tsadar fitarwa a Afirka.[5] Fim din yayi magana akan radadin da yan Neja-Delta ke ciki a Najeriya. A matsayinsa na mawaƙi, shi ne mamallakin El-Montage Records, lakabi rikodin kiɗa.
Rayuwa da matakin Ilimi
gyara sasheAn haifi Thompson a Legas, Najeriya. Ya fito daga jihar Bayelsa, jiha ce a yankin Neja-Delta. Thompson ya sami digiri na farko daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha, Port-Harcourt. Yana auren Funto Diseye Thompson kuma yana da yara uku.[1] [2] [3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ http://www.daylight.ng/daylight nollywood-personality-of-the-day-tarila-thompson Archived 2016-04-12 at the Wayback Machine
- ↑ https://www.pressreader.com/nigeria/thisday/20170225/282033326970800
- ↑ https://www.imdb.com/name/nm2141940/bio