Taoreed Lagbaja
Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja (28 Fabrairun shekarar 1968 - 5 Nuwamba 2024) Laftanar-Janar na Sojojin Najeriya wanda yayi riƙe muƙamin Babban Hafsan Sojojin Najeriya kafin rasuwar sa.[1] Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya naɗa shi a ranar 19 ga watan Yunin shekarar 2023 don maye gurbin Laftanar Janar Faruk Yahaya.[2][3][4] Ya rasu ne a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamban shekarar 2024 a Legas.[5]
Taoreed Lagbaja | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 28 ga Faburairu, 1968 (56 shekaru) |
Sana'a |
Farko-farkon rayuwa
gyara sasheAn haifi Lagbaja a wani gari da ake kira Ilobu na Irepodun jihar Osun a yau a ranar 28 ga Fabrairun shekarar 1968. Ya fara zama a Osogbo inda ya halarci fitacciyar makarantar St Charles Grammar da Kwalejin Malamai na Ƙananan Hukumomi.
Aiki
gyara sasheYa shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya a shekarar 1987 a matsayin memba na kwas na 39 na yau da kullun. An ba shi muƙamin Laftanar na biyu a ranar 19 ga Satumban shekarar 1992 zuwa cikin Rundunar Sojojin Najeriya. A tsakanin shekarar 1992 zuwa 1995, Lagbaja ya kasance kwamandan runduna ta 93. Daga 1995 zuwa 2001, ya kasance kwamandan runduna ta 72 ''Special Forces Battalion''. A shekarar 2001, Lagbaja ya sami digiri na farko a fannin Geography daga Kwalejin Tsaro ta Najeriya. Ya karanta Strategic Studies a Kwalejin Yakin Sojoji ta Amurka a matakin digiri ta biyu.
Ya kasance mai bada umurni a Kwalejin Tsaro ta Najeriya daga 2001 zuwa 2004. A lokacin Lagbaja ya kasance ma’aikaci mai daraja ta 2 mai kula da aikin wanzar da zaman lafiya a hedikwatar rundunar soji ta sashen horar da sojoji da ayyuka. Sannan ya zama darakta a kwamandan rundunar soji da kwalejin ma’aikata ta Jaji daga 2006 zuwa 2009.
A shekarar 2009, ya zama mataimakin shugaban ma’aikata na G1 a hedikwatar 81 Division sannan ya zama kwamanda a bataliya ta musamman ta 72 Makurdi daga 2012 zuwa 2013 da 2014 zuwa 2015. A cikin shekarar 2016, an naɗa shi Shugaban Ma’aikata a Hedkwatar 8 Task Force Division, Monguno. Ya yi aiki a matsayin Darakta na ayyuka a hedkwatar rundunar soji ta sashen horar da sojoji da ayyuka daga Janairu zuwa Disamban shekarar 2018. Ya kasance Kwamandan Hedkwatar 9 Brigade, Ikeja, Jihar Legas da Hedikwatar 2 Brigade, Uyo, Jihar Akwa Ibom. Kafin sabon naɗin nasa, Lagbaja ya kasance babban kwamandan hedikwatar 82 Dibision daga Maris 2021 zuwa Agusta 2022 da Headquarters 1 Dibisha daga Agusta 2022 zuwa Yunin shekarar 2023.
A farkon shekarar 2008, ya halarci kwas na lura da zaman lafiya a Makarantar Sojoji ta Sojojin Najeriya Jaji (Fabrairu – Mayu 2008) da (ECOWAS Standby Force Battalion Command Post Course – Peacekeeping Centre, Bamako, Mali) – (Yuni – Agusta 2010). Ya fara aikinsa a matsayin Laftanar na biyu kuma a halin yanzu shi ne Laftanar Janar, matsayin da aka ƙara masa girma a watan Yulin shekarar 2023.
Lagbaja ya shiga cikin (Operation HARMONY IV) a yankin Bakassi Peninsula; Ofishin Jakadancin Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (MONUC); (Operation ZAKI Tsaro) na cikin gida a jihar Benue; Ofureshan "Lafiya Dole"; Ofureshan MESA/Operation UDO KA – Maris 2021 – Agusta 2022 – (Operation Security) a kudu maso gabashin Najeriya (Anambra/Abia/Ebonyi/Enugu da Imo Jihohin); da kuma (Operation "Saniti" - Aug 2022 zuwa 2023 - Operation Tsaro na Cikin Gida a jihohin Kaduna/Niger.
Rayuwar sa
gyara sasheYa auri Mariya Abiodun-Lagbaja, kuma sunada ƴa-ƴa biyu a tare. Lagbaja yana jin daɗin kallon shirye-shiryen bidiyo da karanta tarihin rayuwa.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Udeh, Stella; Aguwa, Emmanuel; Onwasigwe, Chika (2022). "Workplace burnout and psychological health of military personnel in a Nigerian barrack". Nigerian Journal of Medicine. 31 (3): 302. doi:10.4103/njm.njm_31_22. ISSN 1115-2613. S2CID 250008900 Check
|s2cid=
value (help). - ↑ "Ogalla, Abubakar, Egbetokun, Lagbaja, Musa - Meet Nigeria new Service Chiefs". BBC News Pidgin. Retrieved 2023-06-20.
- ↑ Udeh, Stella; Aguwa, Emmanuel; Onwasigwe, Chika (2022). "Workplace burnout and psychological health of military personnel in a Nigerian barrack". Nigerian Journal of Medicine. 31 (3): 302. doi:10.4103/njm.njm_31_22. ISSN 1115-2613. S2CID 250008900 Check
|s2cid=
value (help). - ↑ Ariemu, Ogaga (2023-06-20). "10 interesting things to know about new COAS, Maj Gen Lagbaja". Daily Post. Retrieved 2023-06-20.
- ↑ Egbas, Jude (6 November 2024). "Chief of army staff Taoreed Lagbaja is dead". thecable.ng. Retrieved 6 November 2024.