Talatu Yohanna (an haife ta ne a ranar 11 ga watan Nuwamba, shekara ta 1973) shugabace kuma yar siyasa. Ta kasance tsohuwar 'yar majalisar wakilan Najeriya inda take wakiltar Mazabar Tarayya ta Demss/Numan/Lamurde a jihar Adamawa.[1][2]

Talatu Yohanna
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
District: Demsa/Numan/Lamurde
Rayuwa
Haihuwa 11 Nuwamba, 1973 (50 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Ayyuka gyara sashe

Yohanna ta fara aiki a matsayin mai kula da harkokin kasuwanci, sannan daga baya ta koma siyasa inda ta yi aiki a matsayin shugabar mata, kansila mai kulawa, mataimaki na musamman sannan kuma mai ba gwamnan jihar Adamawa shawara na musamman. Ta kuma taba zama kwamishinar Kasuwanci da Ma'aikatu a jihar ta Adamawa. Ta kasance tsohuwar 'yar majalisar wakilai ce inda take wakiltar Mazabar Tarayya ta Demsa / Numan / Lamurde, jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress.[3][4] Ta kuma yi aiki a Kwamitin Majalisar Harkokin Mata.

Rayuwar mutum gyara sashe

Honorabul Yohanna tayi aure kuma tana da yara. Yar asalin garin Ngodogoron ce da ke karamar hukumar Lamnurde ta jihar Adamawa. [5]

Manazarta gyara sashe

  1. "Fulani, Iro Dan (18 March 2015). "68 Adamawa candidates vie for National Assembly seats". Premium Times. Retrieved 19 November 2020.
  2. "Ogundipe, Samuel (5 July 2017). "Malabu Scandal: House committee gives reasons why it must summon Goodluck Jonathan". Premium Times. Retrieved 19 November 2020.
  3. "Elumoye, Deji; Oyeyipo, Shola (10 February 2019). "N'Assembly Members in Crucial Popularity Test Next Saturday". This Day Live. Retrieved 19 November 2020.
  4. "Ogunlami, Yinka (20 January 2016). "'My attackers won't go free', Senator says". Pulse Nigeria. Retrieved 19 November 2020.
  5. https://www.manpower.com.ng/people/16657/hon-talatu-yohanna