Tajudeen Abdul-Raheem, (6 Janairu 1961 - 25 Mayu 2009). Ya kasance babban sakatare na kungiyar Pan-African Movement, kuma ya kasance darektan Justice Africa, sannan mataimakin darektan Majalisar Dinkin Duniya Campaign Millennium for Africa na wani shiri na Majalisar, kuma marubuci ne a jaridu daban-daban haka nan da mujallu a duk faɗin duniya akan Afirka.

Tajudeen Abdul-Raheem
Rayuwa
Haihuwa Funtua, 6 ga Janairu, 1961
ƙasa Najeriya
Mutuwa Nairobi, 25 Mayu 2009
Yanayin mutuwa accidental death (en) Fassara
Karatu
Makaranta St Peter's College (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam, Malami da sakatare
Employers Pan-Africanism (en) Fassara
Justice Africa (en) Fassara
United Nations Millennium Campaign (en) Fassara
Kyaututtuka

An haifi Tajudeen a garin Funtua a Jihar Katsina da ke Najeriya a cikin watan Janairu shekarar 1961, kuma ya rasa ran shi a wani hatsarin mota a ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2009 a birnin Nairobi na kasar Kenya, yayin da yake a hanyar zuwa filin jirgin sama domin hawa jirgi zuwa kasar Rwanda inda zai gana da shugaban kasar Paul Kagame. [1]

Ya sami digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa daga jami'ar Bayero, da ke Kano haka nan ya kasance malamin Rhodes a Oxford, ya kuma samu PhD daga jami'ar Buffalo .[2][3]

Manazarta

gyara sashe
  1. http://news.bbc.co.uk/2/hi/africa/8067260.stm
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-08-27. Retrieved 2021-07-15.
  3. https://www.pambazuka.org/governance/tributes-fallen-giant

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe