Suratul Maryam

Sura ta 19 acikin Alqur'ani

Suratul Maryam (Larabci: مريم‎, Maryam ; Larabci ma'anar "Maryama") ita ce surah ta goma sha tara (19)(sūrah) Acikin Al-Qur'ani mai girma ayoyinta 98 (āyāt). Dukkanin surori 114 na cikin Al-Qur'ani an tsara sune daidai da tsarin da aka bi tun lokacin Khalifa Usman. An sanyawa ita wannan surah ta Al-Qur'ani mai girma suna Maryam ne saboda a cikinta an bada labarin Maryamu, mahaifiyar Annabi Isah (Yesu) alaihis salam. A cikinta an ba da labarin abubuwan da suka faru kafin haihuwar Yesu, batun da ke cikin Luka 1 na Baibul ɗin Kirista. Ayoyin cikin surar sun yi bada labaran sanannun annabawa da yawa, wanda suka haɗa da Ishaku, Yakubu, Musa, Haruna, Isma'il, Idris, Adam, da Nuhu.

Suratul Maryam
Surah
Bayanai
Bangare na Al Kur'ani
Suna saboda Maryam a Musulunci
Akwai nau'insa ko fassara Maryam da Maryam
Harshen aiki ko suna Larabci
Full work available at URL (en) Fassara quran.com…
Has characteristic (en) Fassara Surorin Makka

Manazarta gyara sashe