Suleiman Muhammad Adam
Dr. Sulaiman Muhammad Adam (An haife shi ranar 14 ga watan Yuni shekarar 1962), babban limamin Masallacin Sultan Bello dake unguwan sarki Kaduna a halin yanzu. Dakta Sulaiman ya fara jagorantar Sallar Juma'a a Masallacin Sultan Bello a ranar 6 ga watan Janairu shekara ta 2017.[1]
Suleiman Muhammad Adam | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 14 ga Yuni, 1962 (62 shekaru) |
Sana'a |
Karatu
gyara sasheSulaiman yayi karatun firamare a ƙauyen Umoko a Jihar Ribas, kudancin Najeriya. Bayan kammala karatun firamare sai ya zarce zuwa sakandare inda yayi Higher Islamic Studies (H I S) a Jos, a lokacin kuma ya shiga kwalejin Arabic Teachers College Grade 3. Daga nan kuma ya cigaba da karatunsa a kwalejin ilimi ta Kano, inda ya samu shaidar gama karatun NCE. Ya kuma samu shaidar digiri a Madina da kuma Maleshiya, inda ya karanta Larabci, Shari'a da kuma Ilimin Addinin Musulunci. Haka kuma tsohon Lakcara ne a Jami'ar Jihar Kaduna.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ahmadu-Suka, Maryam (6 January 2017). "Suleiman Adam Is New Chief Imam Sultan Bello Mosque Kaduna". dailytrust.com (in Turanci). Retrieved 27 December 2023.
- ↑ "Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Sulaiman Sulaiman". BBC hausa.com. 13 January 2022. Retrieved 27 December 2023.