Suleiman Adokwe

Dan siyasar Najeriya

Suleiman Asonya Adokwe (an haife shi a ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar 1954) an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu a Jihar Nasarawa dake Najeriya, ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekarata 2007.[1] Ɗan jam'iyyar PDP ne. Shi ɗan ƙabilar Alago ne, ƙabilar Idomoid.[2]

Suleiman Adokwe
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 - ga Yuni, 2019 - Umaru Tanko Al-Makura
District: Nasarawa South
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Afirilu, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Nasarawa South
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Nasarawa South
Rayuwa
Haihuwa Jahar Nasarawa, 15 ga Faburairu, 1954 (70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Adokwe ya samu karatun digirinsa na farko a fannin zamantakewa, digiri na biyu a fannin aikin ƙwadago da digirin farko a fannin shari’a, kuma lauya ne. Ya yi aiki da ma’aikatan gwamnatin jihar Nasarawa daga shekarar 1979 zuwa 1999, inda ya kai matsayin sakatare na dindindin, sannan ya kasance kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Nasarawa daga shekarar 2003 zuwa 2006.

Majalisar Dattawa

gyara sashe

Bayan ya hau kujerarsa a Majalisar Dattawa a watan Mayun shekarar 2007, an naɗa shi a kwamitoci a kan Sabis na Majalisar Dattawa, Tsaro da Leƙen Asiri, Sojojin Ruwa, Tsare-tsaren Ƙasa, Man Fetur da Kasuwan Jari.[1] A cikin tantancewar tsakiyar wa’adi na Sanatoci a cikin watan Mayun shekarar 2009, ThisDay ya ce bai ɗauki nauyin wani ƙudiri ba amma ya yi hazaƙa a ƙasa. Adokwe dai mai goyon bayan ƙungiyoyin ƙwadago ne, wanda a cewarsa za su iya ba da kyakykyawan suka ga gwamnati, saboda shugabanninsu na gujewa cin hanci da rashawa da kuma goyon bayan dimokuraɗiyya a cikin ƙungiyoyin.[3]

Adokwe ya sake tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu a jam’iyyar PDP a zaɓen Afrilun shekarar 2011. An zaɓe shi, inda ya samu ƙuri’u 108,844 yayin da Tanko Wambai na jam’iyyar CPC ya samu ƙuri’u 103,320. Wambai yace zai ƙalubalanci sakamakon.[4]

Adokwe ya sake tsayawa takara karo na uku a zaɓen Sanatan Nasarawa ta Kudu a cikin shekarar 2015 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP inda ya sha kaye a zaɓen a hannun Arc Salihu H. Egyebola na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 95,781 yayin da Adokwe ya samu ƙuri’u 91,760.

Bayan kammala zaɓen, Adokwe ya garzaya kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke zamanta a jihar Lafia Nasarawa domin ƙalubalantar nasarar Arc Egyebola. A ranar 12 ga watan Oktoban shekarata 2015 kotun ta yi watsi da ƙarar Adokwe saboda rashin cancanta.

Da rashin gamsuwa da hukuncin, Adokwe ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara a jihar ta Markurɗi Benue, daga bisani kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar zaɓen Sanata Adokwe. Daga nan ne kotun ta umarci INEC da ta mayar da Sanata Adokwe a matsayin zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattawa mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Kudu.

Manazarta

gyara sashe